News
Likita Daya Na Kula Da MarasA Lafiya 33,000 A Kano — Ƙungiyar Likitoci
DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kungiyar likitocin hakori ta kasa ta ce akwai kimanin mutum miliyan 20, amma likitoci 600 ne kawai suke duba su, wanda hakan ke nufin likita ɗaya na kula da marasa lafiya 33,000 a jihar Kano.
Haka zalika Likitocin sun bayyana damuwarsu kan rashin isassun likitocin da za su ke duba marasa lafiya, wanda hakan ya sa suke shirin tafiya yajin aiki daga ranar 1 ga watan Oktoba.
Kungiyar Likitoci Za Ta Shiga Yajin Aiki A Ranar Samun ’Yancin Kai
Ƙungiyar Likitocin ta bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai da sakataren ƙungiyar, Dokta Anas Idris Hassan kamar yanda jaridar NIGERIAN TRACKER ta ruwaito
Ya ce gwamnatin jihar ta amince a watan Yuni za ta biya musu buƙatunsu, amma har yanzu ba ta ɗauki wani mataki ba.
Dokta Anas ya kuma bayyana cewa likitocin da aka ɗauka aiki a watan Satumban 2023 ba su samu albashinsu ba.
Likitocin sun kuma koka kan yanayin asibitocin Kano da rashin manyan kayan aiki.
Babbar matsalar ita ce ƙarancin likitocin da za su ke duba marasa lafiya.
Saboda waɗannan matsaloli, likitocin suka yanke shawarar tafiya yajin aiki daga ranar 1 ga watan Oktoba.
