Connect with us

News

Kungiyar Likitoci Za Ta Shiga Yajin Aiki A Ranar Samun ’Yancin Kai

Published

on

Kungiyar Likitoci Za Su Shiga Yajin Aiki A Ranar Cikar Najeriya Shekara 64 Da Samun ’Yancin Kai

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Kungiyar likitocin hakori ta kasa ta sanya ranar 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar da mambobinta a Kano za su shiga yajin aikin yayin cikar Najeriya shekara 64 da samun ’yancin kai.

Advertisement

Sakataren kungiyar na Kano Dr. Anas Idris Hassan ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kamar yanda jaridar NIGERIAN TRACKER ta ruwaito.

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Muta Ne Bakwai A Matsayin Manyan Shuwagabanni Zartarwa

Dokta Anas ya bayyana cewa duk da yarjejeniyar da suka cimma da gwamnatin jihar Kano watannin da suka gabata  domin biyan bukatunsu, har yanzu gwamnatin ba ta mayar da martani ba.

Advertisement

Dakta Anas ya ci gaba da cewa, sabbin likitocin da suka dauka aiki, wadanda gwamnatin jihar Kano ta dauka aiki a watan Satumbar 2023, ba a biya su albashi ba.

Likitocin sun kuma nuna damuwarsu kan yadda asibitocin Kano ke tabarbare da kuma karancin kayan aiki, inda suka jaddada bukatar gaggauta magance wadannan matsaloli.

Advertisement

Likitocin sun kara cewa ba su da wani zabi illa shiga yajin aikin a ranar 1 ga Oktoba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending