News
An Dakatar Da Wani Likita Bayan Da Ya Je Aiki Ya Yi Mankas Da Giya A Kano
Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta dakatar da wani likita da ke aiki a ɗaya daga cikin manyan asibitoci mallakin gwamnati, saboda tuhumar sa da shan giya yayin da yaje aiki.
A cewar rahotanni, an kai ƙorafin lamarin ga mahukuntan hukumar, inda binciken farko ya tabbatar da cewa likitan ya karya ƙa’idojin aikin likitanci. Wannan ne ya sa aka ɗauki matakin dakatar da shi nan take, yayin da ake ci gaba da bincike mai zurfi kan abin da ya faru.
Gwamnatin Kano Ta Haramta Zuba Yashi Da Sauran Kayan Gini A Kan Titunan Jihar
Sakataren hukumar, Dr. Mansur Mudi Nagoda, ya dakatar Likitan har sai an kammala cikakken bincike, inda yace irin waɗannan halaye sun sabawa ƙa’idojin aiki.
A wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar, Samira Sulaiman, ta fitar, ta ce kula da marasa lafiya na buƙatar cikakkiyar ƙwarewa, musamman a cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati inda rayukan jama’a ke hannun ma’aikatan lafiya.
Ta tabbatar da cewa bincike na ci gaba, kuma za a ɗauki matakan da suka dace da dokokin aikin gwamnati da ƙa’idojin aikin likitanci da zarar an kammala binciken.
