News
Gwamnatin Kano Ta Haramta Zuba Yashi Da Sauran Kayan Gini A Kan Titunan Jihar
Hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano (REMASAB) ta sanar da haramta zuba yashi, dutse, bulo ko ƙasa a kan titunan birnin Kano da kewaye.
Manajan Daraktan hukumar, Dr. Muhammad S. Khalil, wanda ya sanar da haramcin ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da tsafta da kuma hana tare hanyoyi da magudanan ruwa.
Zargin Cin Mutunci Ga ‘Yan Jarida Daga Wasu Jami’an Gwamnatin Kano Na Kara Fitowa
A cewar sanarwar, duk wani ɗan kwangila, mai gina gida ko shago da ke da buƙatar sauke irin waɗannan kayayyaki dole ne ya tanadi ma’aikatan da za su kwashe su nan take bayan saukewa, domin kauce wa cunkoso da barazana ga masu ababen hawa da kuma hana gurbacewar muhalli.
Hukumar ta gargaɗi cewa duk wanda aka samu da saɓawa wannan umarni ta hanyar zuba kayan gini a kan titi ba tare da ɗaukar matakin gaggawa na kwashe su ba, za a ɗauki matakin hukunci a kansa.
REMASAB ta ƙara da cewa za ta yi aiki tare da Kotun Tafida Gidanka wajen hukunta masu laifi, inda hukuncin ka iya haɗawa da tara ko ɗauri, ko kuma duka biyun gwargwadon laifin da aka aikata.
Hukumar ta yi kira ga jama’a da su bi wannan umarni domin tabbatar da tsaftar muhalli da kuma sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa a cikin birnin Kano.
