Sports
Tawagar Super Eagle Ta Makale A Libya.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Biyo bayan nasarar da kungiyar ta samu a filin wasa na Godswill Akpabio a birnin Uyo ta hannun dan wasanta Dele Bashiru, kungiyar ta tashi zuwa kasar Libya inda zatayi wasa a birnin Al-braq.
Sai dai kuma jirginsu bai sauka a birnin na Al-braq ba. Jirgin nasu ya sauka a birnin Benghazi inda zasuyi tafiyar awa biyu zuwa masaukinsu a birnin na Benghazi kuma hukumar wasannin kasar taki basu abun hawan dazai dawo dasu Benghazi.
IKON ALLAH : Wata Tsohuwa ‘Yar Shekara 70 Ta Haifi Santalelen Jariri
Biyo bayan hakan hukumar NFF ta dauki hayar mota domin akawosu Benghazi, amma kuma hukumar filin jirgin ta rife filin jirgin ta hana motar shiga.
Dail Trust ta ruwaito cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto dai babu wata masaniya dangane da fitar tawagar daga filin jirgina Al-braq.
