Connect with us

News

Naira N52 Ake Sayar Da Litar Man Fetur A Kasar Libiya

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Kasar Libiya ta ci gaba da kasancewa ƙasar da ke da farashin man fetur mafi arha a Afrika, inda farashin lita ɗaya na man yake 0.15 Libyan Dinar, wanda ke daidai da kusan dala $0.032 ko kuma ₦52 har a ranar 16 ga Satumba, 2024, kamar yadda Masu bibiyar farashin mai a duniya (Global Petrol Prices) suka ruwaito.

Advertisement

Daily Trust ta ruwaito cewa GPP, wata cibiyar da ke bibiyar farashin man fetur a duniya, ta nuna banbanci mai yawa na farashin man fetur a ƙasashen Afrika. Duk da cewa Libiya tana more mafi arha farashi, ƙasashe kamar Masar, Aljeriya, da Angola suna fuskantar farashi mafi tsada, inda farashin ya kai dala $0.279, $0.342, da $0.351 kowace lita.

Da DUMI-DUMI : INEC Ta Bayyana Okpebolo Na APC A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Edo

A gefe guda, farashin man fetur a Nijeriya ya tashi zuwa N1,000 kowanne lita, yayin da farashin a kasuwar bayan-fage ya kai har N1,600 kowanne lita. Duk da kasancewa mai samar da man fetur, hauhawar farashin man a Najeriya ya haifar da rashin jin daɗin jama’a, musamman bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta yi.

Advertisement

Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ce ke da mafi tsadar man fetur a Afrika, inda farashin ya kai $1.83 kowanne lita. Sauran ƙasashen da ke da farashi mai tsada sun haɗa da Senegal ($1.646), Seychelles ($1.595), Zimbabwe ($1.590), Morocco ($1.527), Uganda ($1.475), da Kenya ($1.453).

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending