Connect with us

News

Shirin Dangote Na Raba Mai Kyauta Zai Kassara Mu – Inji Dallalan Mai

Published

on

Dangote refinery CNG truck 750x430 1

Kungiyar dillalan man fetur a Najeriya, PETROAN, ta bayyana damuwa kan matakin da matatar man Dangote ke shirin dauka na fara raba man fetur da dizal kai tsaye ba tare da bin tsarin dillalai ba.

Shugaban kungiyar, Billy Gillis-Harry, ya bayyana haka a cikin wani shiri na Channels Television a ranar Talata, inda ya ce wannan tsari na iya jefa dubban mutane cikin rashin aikin yi da kuma rusa kasuwancin dillalan mai.

Dalilin Da Ya Sa Ya Mara Wa Tinubu Baya Ba Tare Da Ambaton Shettima Ba —– Shugaban APC Na Arewa Maso Gabas ‎

“Idan kamfani kamar Dangote zai rika kai mai da dizal kai tsaye kyauta ga kwastomomi ba tare da shiga hannunmu ba, to wannan shiri zai kore mu daga harkar,” in ji shi.

A cewarsa, matatar Dangote na shirin fara aikin dakon mai da dizal kyauta daga ranar 15 ga watan Agusta, inda za a kai man kai tsaye ga ‘yan kasuwa da manyan kamfanoni masu amfani da shi.

Matatar, wadda ke tace ganga 650,000 a kowace rana, ta ce ta riga ta sayi sabbin motocin dakon mai masu amfani da iskar gas (CNG) domin aiwatar da shirin.

Kazalika, kamfanin na Dangote ya bayyana cewa masu sayan lita 500,000 za su samu ƙarin lita 500,000 a matsayin rance, wanda za su biya cikin makonni biyu karkashin tsarin bankuna.

Advertisement

Sai dai wannan yunkuri ya jawo ce-ce-ku-ce daga dillalan man fetur da masu harkar sufuri, inda suka ce hakan zai shafi tattalin arzikinsu kai tsaye.

“Dangote na neman mamaye harkar mai gaba ɗaya, hakan zai ruguza rayuwar dubban mutane da ke dogaro da sana’ar man fetur,” in ji wani dillalin mai da ke Abuja.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending