Connect with us

Politics

Dalilin Da Ya Sa Ya Mara Wa Tinubu Baya Ba Tare Da Ambaton Shettima Ba —– Shugaban APC Na Arewa Maso Gabas ‎

Published

on

APC 4

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa mai kula da Yankin Arewa Maso Gabas, Alhaji Mustapha Salihu, ya bayyana dalilin da ya sa ya nuna goyon baya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takara a zaben 2027 ba tare da ambaton Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ba.

Jawabin da Salihu ya gabatar a wajen taron shugabannin jam’iyyar APC na Arewa maso Gabas da aka gudanar a Jihar Gombe, ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu matasa su ka nuna rashin jin daɗi, lamarin da ya kai ga ƙoƙarin kai masa hari.

Advertisement

Iran Ta Sake Ƙaddamar Da Hare-hare Kan Isra’ila

Sai dai a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television, Salihu ya ce an fassara jawabinsa ba daidai ba, kuma kafafen yaɗa labarai sun bayar da rahoton ne ta hanyar da ba ta dace ba.

“Wannan matsala ta samo asali ne daga yadda wasu suka ɗauki sassa na jawabina, ba tare da sauraron cikakken bayani ba. Idan da an saurari jawabina har zuwa ƙarshe, da za a ji yadda na yaba wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, da sauran ‘yan yankinmu da ke cikin gwamnati,” in ji shi.

Advertisement

Ya ce kafin ya nemi shugabannin jam’iyya da su goyi bayan Tinubu a 2027, ya fara ne da gode wa shugaban ƙasar bisa damammakin da ya ba wa yankin Arewa maso Gabas, musamman manyan mukamai da aka bai wa Shettima da wasu.

> “Na ce Shettima ɗanmu ne, kuma muna alfahari da shi. Na kuma bayyana godiyata ga Shugaba Tinubu bisa yadda ya bai wa yankin Arewa maso Gabas muƙamai masu daraja a gwamnatinsa,” in ji Salihu.

Advertisement

Salihu ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa akwai ɓarna ko rashin jituwa tsakanin shugaban ƙasa da mataimakinsa, yana mai cewa hakan ƙage ne da wasu ke yaɗawa domin cimma wata manufa ta siyasa.

“Waɗanda ke ƙoƙarin yaɗa irin waɗannan jita-jita ‘yan kasuwar rikici ne da ke son su cinye jam’iyyar. Harkokin jam’iyya ba a gudanar da su a dandalan sada zumunta ko kafafen yaɗa labarai ba, a ofisoshin jam’iyya ake tafiyar da su bisa tsari da doka,” in ji shi.

Advertisement

Ya kuma jaddada cewa tsarin jam’iyya na zaben fidda gwani bai haɗa da ɗaukar mataimaki ba, domin kuwa, a cewarsa, ana zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa ne kawai, wanda daga baya ke da damar zaɓar wanda zai yi mataimakinsa.

A ƙarshe, Salihu ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da al’umma gaba ɗaya da su guji yaɗa jita-jita, yana mai cewa jam’iyyar APC na nan da tsayin daka kuma babu wata matsala da za ta kawo baraka tsakanin manyan shugabannin gwamnati da jam’iyya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending