News
Ƙarin farashin Man fetur Ya Sa Albashi Mafi Ƙaranci Na 70,000 Ba Shi Da Amfani – Kungiyar NLC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar Ƙwadago ta kasa NLC ta ce za ta sake komawa ga gwamnatin tarayya domin ta ji yadda ma’aikata za su rayu bayan sake kara farashin man fetur a Najeriya.
Kungiyar ta kwadago ta bayyana hakan a ranar Alhamis in da ta ce farashin mai a yanzu haka ya riga ya haɗiye sabon tsarin albashin da gwamnati ta yi alƙawarin bayarwa na naira dubu 70 wanda kuma har yanzu ba a fara bayarwa ba
Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Madatsan Ruwa Biyar Domin Tare Ruwan Dam Ɗin Lagdo
Shugaban ƙungiyar ta NLC, Kwamared Joe Ajaero wanda ya bayyana hakan yayin buɗe wani taron ƙarawa juna sani a Legas ya ce gwamnati ta yaudare su ta hanyar amince wa da naira 70,000 ɗin a matsayin albashi mafi ƙaƙant
Ya kuma shawarci gwamnati da ta magance matsalar yunwa da talauci da damuwar da ƴan Najeriya ke fama da ita tun kafin al’amura su fi ƙarfinsu.a..o0uo:
