News
Jami’an Tsaro Sun Ruga Da Sun Zama Karnukan Farautar Gwamnatin Tarayya— Kungiyar kwadago Ta NLC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta ce Jami’an Tsaro sun ruga da sun zama karnukan farautar gwamnatin tarayya a wannan lokacin.
Sakataren tsare tsaren na kungiyar kwadago ta Najeriya NLC Kwamared Nasir Kabir ne ya baiyyana hakan ya na mai cewa yanzu rundunar Yan Sanda a Najeriya sun ruga da sun zama Karnukan Yan Siyasa.
Kwamared ya ce a yanzu babu wani girmama Dumukradiyyya da Gwamnatin Tarayya take ikirarin cewa tanayi duba da yadda Gwamnatin ke kama Shuwagabanni fararen Hula.
Kwamared Nasir Kabir ya bayyana haka ne a hirarsa da kafar yada labarai ta DCL HAUSA bayan kama Shugaban kungiyar kwadagon Joe Ajaero da kuma afka wa ofishin ƙungiyar kare haƙƙi da sa-ido kan gwamnati, wato SERAP.
Kwamared ya ce shi tabbas bayyi mamakin kama Shugaban kungiyar Kasa ba tunda dai Jami,an Tsaro sun ruga da sun zama yan amshin Shata.
Mun umarci Jami,an tsaro dasu sake mana Shugaban mu idan Kuma hakan ɓata yiwuba tom zamu umarci dukkanin shuwagabannin kungiyoyin kwadago na jihohin 36 dasu zauna a shirin ko ta kwanana domin zamuyi yajin Aikin da ba’ata bayinsaba a Najeriya,Inji sa
Jaridar INDARANKA ta ruwaito cewa safiyar yau Litinin ce hukumar Yan Sandan farin Kaya ta DSS ta kama Shugaban kwadagon Joe Ajearo a filin Jirgin sama dake Abuja zai tafi Kasar Landon domin bikin wayar dakan Yayan kungiyar na Kasashen Duniya.
