News
Gwamnatin Jihar Kano Ta Kashe N555m A Otel, Ta Gaza Kashe Ko Sisi Don Magance Ambaliya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Duk da cewa kimanin mutane arba’in da tara ne aka ce sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Kano, gwamnatin jihar ba ta nuna damuwarta kan kokarin magance ambaliyar ruwa a jihar ba.
SOLACE BASE ta bayyana cewa wannan ya kasance bisa ga cikakkun bayanai na rahoton aikin kasafin kuɗi da gwamnatin jihar ta buga.
Idan dai za a iya tunawa, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ta tabbatar da cewa mutane 49 ne suka rasa rayukansu, yayin da al’umomi 226 suka salwanta sakamakon ambaliyar ruwa da iska a kananan hukumomi ashirin da bakwai na jihar tsakanin watan Janairu zuwa Satumban 2024.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Tudun Wada, Gwale, Wudil, Danbatta, Ajingi, Dala, Gwarzo, Madobi, Bichi, Kano Municipal, Karaye, Tarauni, Minjibir, Bebeji, Rogo, Shanono, Kabo, Garin Malam da Ungogo.
Sauran da aka lissafa sun hada da Kumbotso, Nasarawa, Kura, Dawakin Tofa, Gezawa, Rogo da Bagwai. An kuma lura da cewa ambaliyar ta lalata gidaje 6,583, wanda ya shafi mutane 38,814.
Duk da kasafin Naira miliyan 220 don magance matsalar zaizayar kasa da ambaliyar ruwa a shekarar 2024, ba a kashe naira ku daya ba a cikin watanni shida na farkon shekarar 2024.
Kano dai na da tarihin kashe makudan kudade wajen yaki da zaizayar kasa da kuma shawo kan ambaliyar ruwa.
A kasafin kudi na shekarar 2023, jihar ta yi kasafin Naira miliyan 277 don magance ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, amma an kashe ko sisi don haka a cikin kasafin.
Wani bita da aka yi ya nuna cewa, yayin da jihar ba ta mai da hankali wajen shawo kan ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, ta kashe Naira miliyan 129 wajen biyan alawus na karramawa da cikin watanni shida na farkon shekarar 2024.
Kudin Abinci kai Naira miliyan 33, karbar baki ya kai Naira miliyan 555.
Wannan ci gaban yana zuwa ne tare da miliyoyin Kudin da jihar ke karba a kowane wata a matsayin kudaden muhalli.
An dai nuna damuwa kan yadda jihohi ke kula da kudaden muhalli da ke da nufin magance kalubalen muhalli kamar ambaliyar ruwa da zaizayar kasa.
Mummunan illar da madatsar ruwa ta Alu ta haifar da ambaliya wadda ta yi sanadin salwantar rayuka da dukiyoyin da ta kai biliyoyin Naira a birnin Maiduguri na jihar Borno har yanzu ba a iya tunawa.
