Connect with us

News

Ambaliyar Ruwa  Ta Raba Dubban Mutane Da Gidajensu A Maiduguri

Published

on

Jigawa Ambaliyar Ruwa Tayu Sanadiyar Mutuwar Mutane 16 Tare Lalata Gidaje 3,936 

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Dubban mutane ne suka yi hijira daga gidajensu a wasu sassan Maiduguri a Jihar Borno da ke Nijeriya sakamakon ambaliyar ruwa.

Bidiyoyin da suka rinƙa yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya shanye tituna, mutane na guduwa domin neman mafaka.

Adadin Mutane Da Suka Kamu Da Cutar Kyandar Biri A Najeriya Ya Kai 53 — Hukumar NCDC

Ambaliyar ta tilasta wa dubban jama’a kwana a waje sakamakon yadda ambaliya ta shanye musu gidaje.

Ambaliyar wadda ta soma tun a makon da ya gabata, ta yi ƙamari a ranar Litinin da dare, inda aka wayi garin Talata mutane da dama sun shiga cikin wani hali.

Rahotanni sun nuna cewa ambaliyar ta faru ne sakamakon ɓallewar madatsar ruwa ta Alao da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno.

Advertisement

Tun a ranar Litinin gwamnatin ta Borno ta umarci a rufe makarantu a jihar sakamakon take-taken da gwamnatin jihar ta Borno ta gani na yiwuwar ambaliyar ruwan ta ƙara ƙamari.

Sassan Nijeriya na ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu, wanda dama tuni hukumar hasashen yanayi ta ƙasar ta yi hasashen samun wannan ambaliya.

Ɗaruruwan mutane ne hukumar bayar da agajin gaggawa ta bayar da rahoton sun rasu a ƙasar sakamakon ambaliyar ruwan, jihohin Bauchi da Sokoto da Zamfara da Jigawa na daga cikin jihohin da ambaliya ta fi yi wa ɓarna a ƙasar.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending