News
Kamfanin Telekomm Na Fuskantar Barazanar Rufewa Bayan Ma’aikatansa Sun Fara Yajin Aiki A Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kamfanin Sadarwa na Ƙasa, Telekomm Service na fuskantar barazanar rufewa bayan da ƙungiyar manyan jami’an sadarwa da ma’aikatan sadarwa na ƴan kasuwa suka fara yajin aiki.
Ƙungiyar manyan jami’an ta yi gargaɗin samuwar tseko ga harkokin gudanarwar Kamfanin matuƙar ba a amsa buƙatunsu ba.
Ambaliyar Ruwa Ta Raba Dubban Mutane Da Gidajensu A Maiduguri
Faruwar hakan ka iya jefa miliyoyin masu amfani da ababen sadarwa cikin damuwa a sakamakon rufe kafofinsu.
A ranar Litinin ne aka shiga yajin aikin inda ƙungiyar ta buƙaci a dawo da wasu maaikatanta da aka kora, a ɗaukaka matsayinta, a inganta wajen gudanar da ayyuka da kuma biyan kuɗin mambobi.
A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai, babban sakataren ƙungiyar, Okonu Abdullahi ya ce ma’aikatan da suka tafi yajin aikin su na da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen gudanar da manyan ayyuka a kamfanoni ciki har da IHS da Huawei da sauransu.
Ya ce, daga cikin su akwai injiniyoyi, injiniyoyin sadarwa, injiniyoyin hulɗa da jama’a, da wasu ma’aikata da ke aiki a kamfanonin Telecom sabis.
A kwanakin baya ne cikin watan Afrilu, ƙungiyar ta shiga irin yajin aikin wanda daga bisani ma’aikatar ƙwadago da kamfanonin sadarwa suka sulhunta lamarin.
Daga ƙarshe, ya ce suna ƙoƙarin shawo kan matsalolin duk da cewa ƙungiyar ta ƙi amincewa ta saurare su.
