News
Saurayin Da Ya Zuba Wa Budurwarsa Fetur Sannan Ya Cinna Ma Ta Wuta Saboda Ta Yanke Alaƙarsu Shi Ma Ya Mutu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon saurayin ‘yar wasan Olympics ta Uganda, Rebecca Cheptegei, wanda ya cinna mata wuta, shi ma ya mutu bayan kunar da ya samu a lokacin da ya kai mata hari.
Tsohon saurayin, Dickson Ndiema ya zuba mata fetur ne ya ƙona ta bayan da ta koma gida daga coci a makon da ya gabata.
Kamfanin Telekomm Na Fuskantar Barazanar Rufewa Bayan Ma’aikatansa Sun Fara Yajin Aiki A Najeriya
Rahotanni sun ce ƴar wasan da tsohon saurayin nata sun kasance suna rikici kan wani ɗan karamin fili da ke arewa maso yammacin Kenya, inda take zaune.
Ndiema ya mutu ne a daren ranar Litinin a sashin kula da lafiya da ke Moi Teaching and Referral Hospital, inda aka kwantar.
Advertisements
