News
Masarautar Hadejia: Tarihin Shekaru Dari na Turjiyar Hadejia ya Mamayar Yan Mulkin Mallaka — 1906-2026
Masarautar Hadejia ta sanar da shirinta na gudanar da babban taron tunawa da cika shekaru 120 da yaƙin da al’ummar Hadejia suka yi da Turawan mulkin mallaka a shekarar 1906, wani lamari da ake kallonsa a matsayin muhimmin ginshiƙi a tarihin yankin.
Taron zai gudana ne karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje Haruna, CON, a madadin daukacin al’ummar masarautar.
Kano: Rasuwar Balarabe Nazeephy Ta Bar Babban Giɓi a Aikin Jarida
Da yake jawabi ga manema labarai, Galadiman Hadejia, Alhaji Usman Abdul’aziz, ya bayyana cewa wannan taro ba wai na nishadi kawai ba ne, illa wata hanya ce ta tuna jarumtar kakanni da kuma sadaukarwar da suka yi wajen kare martaba da ‘yancin yankinsu.
Ya ce taron zai bai wa al’umma damar fahimtar ainihin tarihin yaƙin na 1906, tare da ilmantar da matasa kan muhimmancin tsare tarihi da kuma koyo daga darussan da suka gabata.
A cewarsa, daga cikin shirye-shiryen da aka tanada akwai tarukan ilimi da za su mayar da hankali kan yaƙin Hadejia da Turawan mulkin mallaka, inda masana da malamai za su gabatar da muƙalu da bincike kan yadda al’amarin ya gudana da tasirin da ya yi ga yankin.
Ya ƙara da cewa za a fara taron ne a ranar Juma’a, 24 ga Afrilu, 2026, da addu’o’i da ziyartar wuraren tarihi ciki har da kaburburan waɗanda suka rasa rayukansu a yaƙin, domin tuna sadaukarwar da suka yi.
Haka kuma, a ranar Asabar, 25 ga Afrilu, za a ci gaba da tarukan ilimi a Babban Dakin Taro na Makarantar Koyon Aikin Injiniya da Ungozoma da ke Hadejia, inda fitattun masana irin su Farfesa Samaila Suleiman, Farfesa Shehu Tijjani Yusuf da Dr. Junaidu Danlami za su yi bayani kan muhimmancin wannan yaƙi a tarihin Hadejia da Arewa baki ɗaya.
Bayan kammala tarukan ilimi, za a gudanar da Babban Hawan Dawakai (Durbar) karkashin jagorancin Sarkin Hadejia, wanda zai ƙara fito da al’adun gargajiya da kuma martabar masarautar.
Galadiman ya jaddada cewa wannan taro zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin al’umma, tare da ƙara haskaka tarihin Hadejia ga duniya.
A ƙarshe, ya yi kira ga ‘yan jarida da su bayar da cikakken goyon baya wajen yaɗa bayanai kan taron, yana mai cewa tarihin al’umma shi ne ginshiƙin cigabanta da makomarta.
