Connect with us

News

Sama Da Mutane 10,000 Ne Suka Rasa Matsugunansu Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Zamfara.

Published

on

images (8)

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA

Sama da mutane 10,000 ne suka rasa matsugunansu yayin da gonaki da wasu kadarori na miliyoyin naira suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa bayan da aka shafe makonni kadan ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a karamar hukumar Gummi a Jihar Zamfara.

Advertisement

Sarkin Gummi, Mai Shari’a Hassan Lawal (mai ritaya) ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a lokacin da gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya kai ziyarar domin ganewa idanunsa a karamar hukumar Gummi dake jihar.

Gwamnan ya ziyarci garin Gummi da al’ummar Gayari a ranar Asabar domin duba irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi.

Advertisement

Gwamnan ya jajanta wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, sannan ya sanar da bayar da agajin gaggawa na Naira dubu 100, dakuma buhunan kayan abinci dubu 10 tare da gidajen sauro da barguna, ga wadanda ambaliyar ruwa  ta shafa.

Gwamnan ya kuma yi alkawarin magance matsalar ambaliyar ruwan na din-din-din, ta hanyar gina sabbin magudanan ruwa, gyara madatsun ruwa, da yuwuwar gina wasu madatsun ruwan.

Advertisement

Kazalika, yayi alkawarin raba musu filaye nesa da yankin da ke da hadari domin su gina sabbin gidaje.

Hikima Radiyo ta ruwaito cewa mazauna garin Gummi sun nuna jin dadinsu da zuwan gwamnan da kuma yadda ya jajanta musu bayan aika tawaga daban-daban guda uku a baya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending