Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Umarci Ministan Tsaro Da Shugabannin Sojoji Su Tattara Kayansu Su Koma Sokoto Da Aiki

Published

on

Tinubu meets with defence ministers service chiefs 300x200

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, tare da sauran shugabannin rundunar sojoji su tattara kayansu su koma jihar Sokoto a wani yunkuri na kawo karshen aiyukan ta’addancin ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma.

Advertisement

Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da Mista Henshaw Ogubike, darektan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro, ya fitar kamar yanda Jaridar WIKKI TIMES ta ruwaito

Shugabar Kungiyar Matan Jami’an Kwastom Ta Bude Ofishin COWA Reshen PTML

Shakka babu, a halin yanzu, yankin arewa maso yamma ya fi kowanne yanki na Najeriya fuskantar matsalar tsaro inda rahotanni suka bayyana cewa jihohi biyar daga cikin bakwai na yankin sune suka fi samun yawan adadin mutanen da aka yi garkuwa da su a tsakanin 2023 zuwa 2024.

Advertisement

Matsalolin sun fi tsamari a jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, sai kuma jihar Sokoto wacce ke biye musu baya musamman a bangaren yawan garkuwa da mutane da kuma kai hare-hare a kan farar hula da jami’an tsaro a wasu lokutan.

Sanarwar komawar Ministan da Shugabannin rundunar sojoji na zuwa ne kasa da kwanaki biyu bayan wani faifan bidiyo ya nuna yadda wasu ‘yan bindiga a jihar Zamfara suka kone wasu motocin sojoji guda hudu bayan sun kwashe makamai da sauran kayan aikin sojoji dake cikin motocin na musamman.

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta nuna bacin ranta a kan yadda ‘yan bindiga a yankin arewa ke kara samun karfin gwuiwa tare da bayyana cewa ta dauki wannan mataki ne domin kawo karshen matsalar tsaro tare da dawo da zaman lafiya a yankin.

Matawalle ya bayyana cewa, yayin zamansu a yankin arewa maso yamma, zasu jagoranci tsara kai hare-haren da zasu kai ga an samu nasara a kan shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, tare da yaransa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending