Connect with us

Labarai

Adadin ‘Yan Najeriya Da Amurka Ke Shirin Kora Ya Kai 157

Published

on

images (14)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) ta ƙara wasu ‘yan Najeriya 24 cikin jerin mutanen da take shirin kora daga ƙasar, lamarin da ya kai adadin ‘yan Najeriya da ke cikin jerin zuwa 157.

DHS ta bayyana hakan ne a shafinta na intanet, inda ta wallafa sunayen mutanen ƙarƙashin wani kundin bayanai mai suna “Worst of the Worst”, wanda ke ɗauke da bayanan baƙin haure da hukumomin Amurka ke zargi da aikata manyan laifuka.

Jami’an Tsaro Su Guji Yin Barazana Ga  Yan Jaridu Yayin Gudanar Da aikinsu  ‎—Ministan Yada Labarai

A cewar ma’aikatar, sababbin mutanen da aka ƙara cikin jerin na fuskantar zarge-zarge da suka haɗa da damfara ta intanet, safarar ƙwayoyi, safarar kuɗaɗen haram, satar shaidar ɗan ƙasa, cin zarafi da kuma muzguna wa yara.

Daga cikin waɗanda aka saka cikin jerin akwai Emmanuel Omowaiye, wanda aka kama a Richmond, Texas, bisa zargin damfara ta hanyar aika saƙonni; Laurene Onwuka a Chantilly, Virginia, kan zargin sojan gona; da Olusegun Shonekan a Newark, New Jersey, bisa zargin damfara ta intanet.

Sauran sun haɗa da Olusegun Olaseni a Indiana, Peter Ude a Georgia da Newton Jemide a New Jersey, waɗanda ake zargi da laifuka daban-daban da suka shafi damfara da safarar miyagun ƙwayoyi.

Advertisement

Haka kuma, jerin ya ƙunshi Shedrack Umukoro, Olasoji Akinbode, Oluwatosin Afolabi, Alameen Adetunji Tokosi, Joshua Ipoade da Michael Orji, waɗanda aka kama a jihohin Mississippi, New Jersey, Texas, Illinois, Georgia da Wisconsin.

Sauran ‘yan Najeriya da aka ambata sun haɗa da Ahmadu Apooyin, Teslim Kiriji, Onomen Uduebor, Charles Ochi, Daniel Eta, Ifeanyi Ibennah, Kazeem Runsewe da Fatiu Lawal.

Haka kuma, akwai Justin Akubueze, Moyinoluwaseun Okeowo, Babajide Oluwaseun Faseyi da Bright Eigbedion, waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da damfara, sata, cin zarafi da safarar kuɗaɗe.

Matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Donald Trump na ƙara tsaurara matakan shige da fice tare da korar baƙin haure da hukumomi ke zargi da aikata manyan laifuka daga Amurka.

Sai dai, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ma’aikatar ba ta bayyana ranar da za a fara korar ‘yan Najeriya da ke cikin jerin ba.

 

Advertisement

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending