Connect with us

News

Rashin Adalci Ne Babban Ƙalubalen Da Najeriya Ke Fuskanta  —Shugaban Majalisar Dattawa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana rashin adalci a matsayin babban ƙalubalen da Najeriya ke fama da ita.

Advertisement

Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom a yayin addu’ar nuna farin cikin na ɗaga darajar mai shari’a Festus Ntong, zuwa kotun ɗaukaka ƙara bayan bayan shafe tsawon shekaru yana hidimta wa jihar ta Akwa-Ibom.

Kotu Ta Tasa Ƙeyar Mahdi Shehu Zuwa Gidan Gyaran Hali

A cewar sanarwar da mai taimaka wa sanatan na musamman kan yaɗa labarai, Akpabio ya ɗora alhakin matsalar tsaron da Najeriya ke fama da shi ne kan rashin adalci inda ya ce ba ƙasar da za ta zauna lafiya matuƙar akwai rashin adalci.

Advertisement

“Babbar matsalar Najeriya ita ce rashin adalci. Duk inda ba adalci, ba za a samu zaman lafiya ba. Ina addu’ar ubangiji ya cigaba da riƙo da hannun alƙalanmu wajen tabbatar da adalci a Najeriya da ma duniya bakiɗaya,” in ji shi.

Akpabio ya buƙaci alƙalai da su yi amfani da ofisoshinsu wajen wajen tabbatar da adalci ga wanda aka zalunta.

Advertisement

Sannan ya bayyna mista Ntong a matsayin jarumi wanda ya yi zama na daban cikin abokansa alƙalai tare da roƙonsa kan ya cigaba da riƙo da waɗannan kyawawan abubuwa.

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending