News
NDLEA Ta Kama Mutane 1,345 Da Wasu Muggan Kwayoyi A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta ce ta kama mutane 1,345 da ake zargi, sannan ta kuma kama wasu haramtattun kwayoyi masu nauyin kilogiram 8,430,239 a shekarar 2024.
Kwamandan Hukumar na jihar, Abubakar Idris-Ahmad, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 02 ga Janairu 2025, yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Kano.
Rashin Adalci Ne Babban Ƙalubalen Da Najeriya Ke Fuskanta —Shugaban Majalisar Dattawa
Ya ce wadanda ake zargin sun hada da maza 1,301 da mata 44.
Idris-Ahmad, ya ce haramtattun abubuwan da aka kama sun hada da hemp, hodar iblis, heroin, methamphetamine, codeine, da kwayar tramadol sama da miliyan biyar.
Ya ce rundunar ta kuma kama wasu mutane 128 da aka kama da laifuka daban-daban da suka shafi muggan kwayoyi.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
