News
NDLEA Ta Kama Mutane 22, Ta Kwato Miyagun Kwayoyi Da Makamai A Kano
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen jihar Kano, ta cafke mutane 22 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi tare da kwato makamai da wasu kayayyakin a wani gagarumin samame da ta kai a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Malam Sadiq Muhammad-Maigatari, ya bayyana cewa samamen ya gudana ne a ranar 10 ga Afrilu, inda ya mayar da hankali kan wuraren da ake zargi da safarar kwayoyi kamar Dan’agundi, Gwangwazo, Farm Center (kan hanyar Zaria), Tashar Rami da Filin Idi.
ADG Care Foundation Ta Kaddamar Da Tallafi A Makarantun Sakandare 13 A Kano
A cewarsa, kayayyakin da aka kwato sun hada da tabar wiwi (cannabis sativa), “suck and die”, maganin roba (rubber solution), da makamai daban-daban da ake zargin an mallaka ba bisa ka’ida ba.
Kwamandan NDLEA na jihar Kano, Malam Abubakar Idris-Ahmad, ya bayyana cewa wannan samame na daga cikin kokarin hukumar na dakile yaduwar miyagun kwayoyi da safararsu, musamman ganin yadda hakan ke barazana ga lafiyar al’umma da zaman lafiya.
Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da bincike don gano sauran wadanda ke da hannu a cikin harkar, tare da tabbatar da gurfanar da su a gaban kotu idan an kammala bincike.
A gefe guda kuma, wadanda aka kama da laifin amfani da kwayoyi za a tura su zuwa cibiyoyin gyara halayya domin samun kulawa da taimako na musamman, bisa tsarin hukumar.
NDLEA ta kuma bukaci hadin kan al’umma wajen bayar da rahoton duk wata alama ko shakku da suka gani game da safarar miyagun kwayoyi a yankunansu.
