News
Yan Siyasa Sun Karkatar Da Naira Biliyan 360 Daga Lalitar Gwamnati Sun Sayi Kadarori A Amurka — Rahoto
Wani rahoton ƙungiyar da ke binciken cin hanci da rashawa ya ce wasu manyan ’yan siyasa da jami’an gwamnati a Nijeriya sun karkatar da daruruwan miliyoyin daloli daga dukiyar gwamnati cikin tsawon shekaru 30, sannan suka karkatar da kuɗin zuwa sayen kadarori 284 a Amurka.
Rahoton ya ce cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a Nijeriya, ɗaya daga cikin ƙasashe mafi girman tattalin arziƙin Afirka kuma ƙasar da ta fi kowace ƙasa a nahiyar samar da man fetur.
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
Wannan bincike ya sake dawo da batun cin hanci da rashawa kan gaba, watanni kaɗan gabanin zaɓen shugaban ƙasa na watan Janairu, wanda ake sa ran matsin tattalin arziƙi da ƙara tabarbarewar tsaro za su kasance daga cikin manyan batutuwan da za su mamaye zaɓen.
Tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023, Shugaba Bola Tinubu, wanda zai nemi sake zaɓe, ya bayyana yaƙi da cin hanci da rashawa a matsayin ɗaya daga cikin manufofinsa. Sai dai manyan shari’o’in cin hanci da rashawa na tafiyar hawainiya a kotuna.
A cikin rahoton da ƙungiyar Platform to Protect Whistleblowers in Africa (PPLAAF) ta wallafa a ranar Talata, ta ce ta gano kadarori 284 a Amurka, waɗanda jimillar darajarsu ta kai kusan dala miliyan 271 kwatankwacin ₦360.37 biliyan., kuma aka danganta su da jami’an Nijeriya 61, ciki har da waɗanda ke kan mulki da waɗanda suka taɓa riƙe manyan mukamai.
Binciken, wanda ya duba kadarorin da aka saya tun bayan komawar Nijeriya mulkin farar hula a shekarar 1999, ya kuma yi zargin cewa yaƙin da ake yi da ta’addanci ya ci gaba da samar da damar samun kuɗi ga wasu daga cikin “manyan jami’an soji.”
Rahoton ya ce fiye da rabin kadarorin an saya su ne a lokacin da jami’an ke kan mukami, “a daidai lokacin da suke da mafi girman damar amfani da albarkatun gwamnati da tasirinsu.”
PPLAAF ta ce daga cikin mutane 61 da ta bincika, 39 daga cikinsu an riga an zarge su a bainar jama’a, an gurfanar da su ko kuma an same su da laifin cin hanci da rashawa.
Rahoton ya ce an sayi mafi yawan kadarorin ba tare da karɓar rancen jinginar gida ba, abin da ya ce na iya zama “alamar damuwa game da halatta kuɗin haram.”
Sai dai PPLAAF ta ce haɗin gwiwar ƙasashen duniya da zai taimaka wajen ƙwace irin waɗannan kadarori har yanzu yana da iyaka.
Daga cikin jami’an da PPLAAF ta ambata akwai ’yan majalisa da jami’an gwamnatocin jihohi da kuma hukumomin tsaro.
Binciken ya gano cewa mafi yawan kadarorin da aka gano jami’an ɓangaren tsaro ne suka saya.
PPLAAF ta ce yawan kuɗaɗen da ake kashewa a harkokin tsaro da yaƙi da Boko Haram ya haifar da damar yin kwangiloli ba tare da cikakken bayani ga jama’a ba.
Rahoton ya ambaci wasu manyan jami’an da tuni suke fuskantar tuhume-tuhume, ciki har da wani da ake zargi da mallakar kusan kadarori 20 a Amurka.
PPLAAF ta ce kadarorin da aka gano a binciken “bai kai ya kawo ba idan aka kwatanta da almundahanar da ake tafkawa,” domin suna nuna lalacewar tsarin ilimi da asibitocin da ba su da isassun ma’aikata, da kuma wutar lantarki da aka kasa samarwa.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nijeriya, EFCC, da masu magana da yawun shugaban ƙasa ba su mayar da martani ga buƙatar kamfanin dillancin labarai na AFP ba.
