Sports
Masoya kwallon kafa bakwai Sun mutu, wasu da dama kuma suka jikkata a hatsarin mota a Brazil
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.
Akalla mutane bakwai ne suka mutu yayin da wasu 27 ke kwance a asibiti jiya Lahadi a kudu maso gabashin Brazil, lokacin da wani direba ya rasa iko da wata motar safa da ke dauke da ‘yan wasan kwallon kafa a kan wata hanya mai tsaunuka, a kasar Brazil.
Hatsarin ya faru ne a wata babbar hanya da ke kusa da Belo Horizonte a jihar Minas Gerais, in ji su.
Juyin Mulkin : ECOWAS ta Yi Fatali da Shirin Mika Mulki Har Tsawon Shekaru Uku.
Fasinjojin da kafar yada labarai ta G1 ta zanta da su, sun ce direban ya yi kukan cewa ba shi da birki jim kadan kafin ya rasa yadda zai yi.
Fiye da magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Korintiyawa 40 da na Sao Paulo ne ke cikin motar bas, suna dawowa daga wasan da suka yi a daren jiya a Belo Horizonte.
Fernando Frois, Laftanar da ma’aikatan kashe gobara na Minas Gerais, ya ba da rahoton adadin wadanda suka mutu amma bai bayyana irin yanayin da wadanda ke kwance a asibiti suke ba.
Hukumar kula da zirga-zirgar kasa ta kasar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce motar ba ta da rajista kuma ba ta da izinin jigilar fasinjoji tsakanin jihohi.
Kungiyoyi daga sassan Brazil, da kuma hukumar kwallon kafa ta Brazil, sun mika ta’aziyyarsu ga iyalai da abokanan wadanda lamarin ya shafa.
AFP
