News
An Cafke Mutane Hudu Kan Zargin Rushe Aji da Sayar da Kayan Ginansa A Kano
Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta kama mutane hudu bisa zargin rushe wani aji a Makarantar Firamare ta Unguwar Uku da ke Karamar Hukumar Tarauni, tare da sayar da kayan ginin ajin.
Shugaban hukumar, Malam Saidu Yahaya, ya bayyana hakan a lokacin da yake magana kan binciken da hukumar ke gudanarwa bayan wasu mazauna yankin sun shigar da korafi kan rushewar ajin.
Matasan Gawuna Sun Sauya Sheka, Sun Goyi Bayan Gwamna Abba
A cewar Yahaya, binciken farko ya nuna cewa ana zargin shugaban makarantar ya hada baki da wasu mambobin Kwamitin Gudanar da Makarantu na Al’umma (SBMC) da kuma Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Tarauni wajen rushe ajin.
Ya ce ana zargin wadanda ake tuhuma da sayar da karfe da kayan rufin ajin bayan rushe shi, ba tare da samun sahalewar hukumomin da abin ya shafa ba.
Shugaban PCACC ya ce an kama mutane hudu dangane da lamarin, inda ya kara da cewa za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala binciken.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wani yunkuri na lalata ko karkatar da kadarorin gwamnati da na al’umma, domin daukar matakinda ya dace.
-
Uncategorized6 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days ago
Aƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
-
News1 day ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
