Connect with us

News

Ba Na Siyasa Bisa Son Kai, Abin da Gwamna Abba Ya Ce Nake Yi —Waiya

Published

on

img 0773 (1)

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin uban gidansa a siyasance, yana mai cewa ba ya ɗaukar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin uban gidansa na siyasa.

Waiya ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da shugabanni da matasan ƙungiyar Abba Door-to-Door ta Jihar Kano.

Cutar Mashako Ta Hallaka Yara Sama Da 50 A Kano 

Kwamishinan ya ce ba shi da wani uban gida a siyasa face Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa duk abin da gwamnan ya umurce shi da yi shi yake aiwatarwa.

«“Wallahi tallahi, ban san kowa a siyasa ba sai Gwamna Abba Kabir Yusuf, kuma shi ne uban gida na, ba Kwankwaso ba,” in ji Waiya.»

Ya kuma karyata rahotannin da ke cewa yana da niyyar neman kujerar ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Dala a zaɓen 2027, amma ya fuskanci tangarda.

Advertisement

Waiya ya ce bai taɓa bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Dala ba, yana mai jaddada cewa harkokinsa na siyasa suna tafiya ne bisa abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umurce shi.

«“Ni ban taɓa cewa zan yi takarar Dala ba. A siyasata, sai abin da Gwamna Abba ya ce da ni,” in ji shi.»

Kwamishinan ya ce babban burinsa a halin yanzu shi ne ganin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu nasara a zaɓen 2027, domin ya ci gaba da jagorantar Jihar Kano.

Ya ce zai ci gaba da mara wa gwamnatin Abba Yusuf baya tare da yin aiki wajen ganin manufofin gwamnatin jihar sun samu nasara.

Kalaman na Waiya na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar Kano ke ƙara ɗaukar sabon salo gabanin babban zaɓen 2027, musamman dangane da makomar alaƙar siyasa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon Gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Waiya ya jaddada cewa ba ya siyasa bisa son kai ko wata buƙata ta neman mukami, illa dai yana aiki ne bisa umarnin da yake samu daga Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending