News
An Daure Matashi Shekaru 10 Bayan Amfani Da ChatGPT Wajen Shirya Fashin Banki
Wata kotun tarayya a Amurka ta yanke wa wani matashi mai shekaru 23, Deron Lewis-Payne, hukuncin zaman gidan yari na watanni 121, wato shekaru 10 da wata daya, bayan samunsa da laifin fashin banki da kuma amfani da bindiga wajen aikata laifin.
Lewis-Payne, mazaunin Omaha a jihar Nebraska, ya aikata fashin ne a ranar 10 ga Fabrairu, 2026, lokacin da ya shiga bankin i3Bank dauke da bindiga.
Dino Melaye Ya Yi Barazanar Maka Shugaban Hukumar Haraji Ta Kasa A kotu
A cewar Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, matashin ya nufi ma’aikatan bankin da bindigar, inda ya yi musu barazanar kashe su idan ba su bi umarninsa ba.
Daga bisani, ma’aikatan sun ba shi kusan dala 9,175 da ke cikin bankin kafin ya tsere.
Binciken jami’an tsaro ya gano cewa Lewis-Payne ya yi amfani da ChatGPT wajen taimaka masa wajen shirya fashin. An gano a wayarsa tambayoyin da ya yi wa manhajar kan yadda jami’an tsaro ke daukar lokaci kafin su isa wurin da aka aikata laifi, da kuma wasu bayanai da suka shafi bindigar da kuma samun harsasai.
Jami’an tsaro sun kuma gano cewa tarihin Google Maps na wayarsa ya nuna cewa ya nemi hanyar zuwa bankin i3Bank kafin aikata fashin.
Bayan fashin, hotunan kyamarorin tsaro sun taimaka wajen gano shi, yayin da bayanan wasu shaguna suka nuna cewa ya yi amfani da wani bangare na kudin wajen sayen takalma da tufafi.
Jami’an tsaro sun kuma gano motar da ake zargin ya yi amfani da ita wajen fashin, tare da wasu daga cikin kayayyakin da ya saka a lokacin aikata laifin.
Kotun ta yanke masa watanni 37 a gidan yari kan laifin fashin bankin, sannan ta kara masa watanni 84 saboda nuna bindiga yayin aikata laifin. Za a yi hukuncin ne a jere, wanda ya kai jimillar watanni 121.
Daga cikin kudin da aka sace, jami’an tsaro sun samu dala 2,397, yayin da ba a gano bindigar da aka yi amfani da ita ba.
Bayan kammala zaman gidan yari, Lewis-Payne zai kasance karkashin kulawar hukuma na tsawon shekaru biyar.
Hukumar FBI ce ta jagoranci binciken lamarin.
