Connect with us

News

Aƙalla Mutane Biyar Ne Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Rikici A Tashar Mota 

Published

on

Aƙalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a wani rikici da ya ɓarke a Garejin Naira da Kwabo da ke Ikire, Ƙaramar Hukumar Irewole ta Jihar Osun.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa rikicin ya faru ne ranar Litinin, bayan da wasu da ake zargin ’yan dabar siyasa ne suka yi ƙoƙarin ƙwace ragamar jagorancin garejin.

Dino Melaye Ya Yi Barazanar Maka Shugaban Hukumar Haraji Ta Kasa A kotu

Majiyar ta ce uku daga cikin mutanen da suka mutu direbobin motocin haya ne da ke gudanar da harkokinsu a garejin, yayin da ba a samu cikakken bayani kan sauran mutum biyun ba.

An ce rikicin ya samo asali ne daga takaddamar da ta daɗe tsakanin ɓangarori biyu na Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW), kan wanda zai jagoranci reshen ƙungiyar a Ƙaramar Hukumar Irewole.

Rikicin ya jefa yankin cikin fargaba, inda wasu ’yan kasuwa suka rufe shagunan su tare da barin wurin domin tsira da rayukansu.

Advertisement

Kafin rikicin ya tsananta, Babban Jami’in ’Yan Sandan Ikire, DPO Olatona Bamidele, ya jagoranci jami’an ’yan sanda zuwa garejin domin ƙarfafa tsaro.

Sai dai, har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun da ke Osogbo ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending