Connect with us

News

Mataimakin Shugaban Jami’ar Atiba Ya Sha Da Kyar Bayan Zanga-zangar Dalibai

Published

on

IMG 20260825 235828 695

Mataimakin Shugaban Jami’ar Atiba da ke Jihar Oyo ya tsere ta katanga yayin da rikici ya ɓarke tsakanin jami’ar da ɗaliban shari’a kan dakatar da jami’ar daga koyar da fannin shari’a.

Lamarin ya faru ne bayan Hukumar Kula da Ilimin Shari’a ta Najeriya ta dakatar da jami’ar daga karɓar sabbin ɗaliban shari’a da kuma koyar da darussan shari’a na tsawon shekaru 10.

An Cafke Mutane Hudu Kan Zargin Rushe Aji da Sayar da Kayan Ginansa A Kano ‎

Bayan sanar da matakin, ɗaliban shari’a na jami’ar sun gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin amincewarsu da dakatarwar, tare da neman a fayyace musu makomar karatunsu.

Rahotanni sun ce rikicin ya ƙara tsamari ne yayin da Mataimakin Shugaban Jami’ar ke magana kan dalilan da suka sa aka dakatar da cibiyar.

An ruwaito cewa ya danganta dakatarwar da rashin cika wasu sharuɗɗan da Hukumar Kula da Ilimin Shari’a ta Najeriya ta gindaya domin jami’a ta ci gaba da koyar da shari’a.

Advertisement

Sai dai bayan kalaman nasa, lamarin ya rikide zuwa hayaniya yayin da wasu ɗalibai suka nuna fushinsu, abin da ya haifar da rikici a harabar jami’ar.

A yayin rikicin ne, rahotanni suka ce Mataimakin Shugaban Jami’ar ya tsere daga wurin ta hanyar ƙetare katanga.

Ɗaliban sun bayyana cewa zanga-zangar tasu ba ta wuce neman a saurari koke-kokensu da kuma samun cikakken bayani kan makomar karatunsu ba, bayan dakatar da jami’ar daga koyar da shari’a.

 

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending