Connect with us

News

“Ba za Mu Bayar Da Ko Taku Daya Na Kasa Ba  Don Yin Burtali Ga Fulani Makiyaya” —Gwamnan Jihar Benue

Published

on

hyacinth alia 1

Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi watsi da ƙudurin samar da burtalai ba tare da amincewar gwamnatinsa da al’ummar jihar ba.

Hakan na zuwa ne a lokacin da ake ƙoƙarin yin doka dangane da batun, bisa ƙudurin Gwamnatin Tarayya na samar da burtalai wanda aka sanya jihar ta Benue a rukunin farko.

An Cafke Mutane Hudu Kan Zargin Rushe Aji da Sayar da Kayan Ginansa A Kano ‎

Sai dai a yayin da ya ke jawabi wajen wani taron al’umma da ya ƙunshi mutane daga ƙananan hukumomin Katsina-Ala, Ukum da Logo, gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci bayar da ko da taku ɗaya na ƙasar jihar ga makiyaya don yin burtali ba tare da amincewarsu ba.

Gwamnan ya kuma soki batun janye dakatar da yawon kiwon dabbobi, inda ya ce hakan ne kawai zai magance rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Gwamna Alia ya ƙara da cewa gwamnatinsa na ci gaba da ƙoƙarin inganta tsaro a yankin Sankere, inda ya sanar da tura rundunonin sojoji zuwa sassa uku a yankin.

Advertisement

Ya ce za a girke rundunar jami’an a yankunan Agu da ke Katsina-Ala, Anyiin da ke Logo, sai kuma Azendeshi da ke Ukum. Sannan ya ce za a raba babura masu ƙafa biyu guda 30 ga jami’an tsaro domin sauƙaƙa ayyukan sintiri da kai ɗaukin gaugawa.

Gwamnan yanzu haka na gudanar da rangadin yin godiya ga masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC, sakamakon zaɓarsa a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar a babban zaben shekarar 2027 da ke tafe.

 

 

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending