News
Kamfanin OPay Ya Karyata Jita-jitar Dakatar Da Ayyukansa
Kamfanin OPay ya karyata wani saƙon bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke cewa kamfanin zai dakatar da ayyukansa daga ranar 1 ga Satumba, 2026.
Saƙon ya yi ikirarin cewa OPay za ta dakatar da ayyukanta daga ranar, tare da umartar kwastomominta da su cire kuɗaɗensu daga asusun ajiyarsu.
Sai dai kamfanin ya ce saƙon ba gaskiya ba ne, yana mai tabbatar da cewa babu wani shiri na dakatar da ayyukansa daga 1 ga Satumba.
OPay ta ce ayyukanta na ci gaba da gudana yadda ya kamata, inda ta buƙaci kwastomominta da su kwantar da hankalinsu tare da yin watsi da saƙon.
Kamfanin ya kuma shawarci jama’a da su riƙa tabbatar da sahihancin bayanai kafin su yaɗa su a kafafen sada zumunta, musamman bayanan da suka shafi kuɗi.
OPay ta ce kwastomominta su dogara da sanarwar da kamfanin ke fitarwa ta hanyoyin sadarwarsa na hukuma domin samun sahihan bayanai.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun yaɗuwar saƙonnin ƙarya a kafafen sada zumunta, lamarin da kan jefa jama’a cikin ruɗani da fargaba.
Saboda haka, kamfanin ya buƙaci masu amfani da ayyukansa da su yi watsi da saƙon tare da ci gaba da amfani da ayyukan OPay kamar yadda suka saba.
