News
Ƙungiyar MURIC Ta Yi Allah-wadai Da Hana Ɗalibai Musulmi Sanya Hijabi A Makarantar OAU
Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Muslim Rights Concern (MURIC) ta yi Allah-wadai da rahoton hana wasu ɗalibai mata Musulmi sanya hijabi a International School da ke ƙarƙashin Obafemi Awolowo University (OAU), Ile-Ife.
MURIC ta ce ɗaliban sun kwashe wasu kwanaki ba sa zuwa makaranta bayan an bukace su da su cire hijabin kafin a ba su damar shiga harabar makarantar.
Kamfanin Amurka Ya Maka Shugaba Tinubu Da Gwamnatin Najeriya A Kotu, Sun Nemi Diyyar Dala Miliyan 57
Daraktan Zartarwa na ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce matakin ya saba wa ’yancin addini da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.
A cewar MURIC, daga bisani ɗaliban sun koma makaranta ba tare da hijabi ba, bayan an sanar da su cewa Majalisar Gudanarwar OAU ba za ta tattauna batun ba sai taronta na Disamba 2026.
Ƙungiyar ta yi kira ga mahukuntan OAU da na makarantar da su mutunta ’yancin ɗaliban na gudanar da addininsu.
MURIC ta kuma buƙaci a cire abin da ta kira takunkumin sanya hijabi nan take ba tare da wani sharadi ba, tana mai cewa Sashe na 38 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya kare ’yancin tunani, lamiri da addini.
Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, mahukuntan OAU da International School ba su fitar da martani kan zargin ba.
