Uncategorized
Kamfanin Amurka Ya Maka Shugaba Tinubu Da Gwamnatin Najeriya A Kotu, Sun Nemi Diyyar Dala Miliyan 57
Wani kamfanin Amurka, Von Batten-Montague-York, ya shigar da ƙara a kan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da gwamnatin tarayya, yana neman diyyar da ta kai dala miliyan 57.
Kamfanin ya kuma shigar da ƙarar ne a kan tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, da kamfanin DCI Group.
Ronaldo Ya Ce Bai Yi Murabus Daga Buga Wa Portugal Wasa Ba
A cewar kamfanin, ya shigar da ƙarar a Kotun Tarayya da ke Washington, D.C., a ranar 28 ga Satumba, 2026, bisa zargin ɓata sunan shugaban kamfanin, Dr Von Batten, da kuma wata makarkashiyar sace shi da cutar da shi.
Kamfanin ya ce yana neman dala miliyan 36 daga Shugaba Tinubu da gwamnatin Najeriya, dala miliyan uku daga Fani-Kayode, sannan dala miliyan 18 daga DCI Group.
Von Batten-Montague-York ya ce dalilin da ya sa bai bayyana ƙarar tun da farko ba shi ne saboda ana kan miƙa takardun ƙarar ga waɗanda aka shigar da ƙarar a kansu, kamar yadda dokokin Amurka suka tanada a shari’o’in da suka shafi gwamnatocin ƙasashen waje.
Sai dai kamfanin ya amince cewa ƙarar da ya shigar kan Tinubu da gwamnatin Najeriya na iya fuskantar ƙalubalen shari’a, saboda dokar Amurka da ke bai wa gwamnatocin ƙasashen waje kariya daga wasu nau’ukan ƙara.
A halin yanzu, zarge-zargen da kamfanin ya gabatar a gaban kotu dai zarge-zarge ne kawai, kuma ba a tabbatar da su a matsayin gaskiya ba.
