Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Satar Adaidaita Sahu A Kano

Published

on

IMG 20261007 WA0001

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da fashi da makami, tare da kwato Adaidaita Sahu da ake zargin sun yi wa direbansa fashi.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya faru ne bayan wani mai suna Nasiru Ibrahim ya kai rahoton satar Adaidaita Sahunsa.

Ƙungiyar MURIC Ta Yi Allah-wadai Da Hana Ɗalibai Musulmi Sanya Hijabi A Makarantar OAU

A cewar Kiyawa, waɗanda ake zargin sun yi hayar Adaidaita Sahun ne daga Hotoro Quarters zuwa Yar Gaya da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, kan kuɗin haya naira 8,000.

Ya ce yayin da suke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, mutanen sun fito da bindigogi ƙirar gida, suka yi wa direban barazana tare da kwace Adaidaita Sahun, sannan suka ja shi zuwa wani daji inda suka bar shi kafin su tsere.

Kakakin rundunar ya ce bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, jami’an Sashen ’Yan Sandan Filin Hockey sun gudanar da binciken sirri, inda a ranar 3 ga Oktoba suka gano Adaidaita Sahun a kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, a Ƙaramar Hukumar Wudil.

Advertisement

Ya ce jami’an sun kuma kama Abubakar Isah, mai shekaru 27, da Shehu Ibrahim, mai shekaru 25, waɗanda dukkansu mazauna ƙauyen Zogarawa ne da ke Dawakin Kudu.

A yayin samamen, rundunar ta ce ta kwato bindigogi ƙirar gida guda biyu daga hannun waɗanda ake zargin.

CSP Kiyawa ya ce waɗanda ake zargin sun amsa laifin yayin gudanar da bincike, inda ya ƙara da cewa za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

Rundunar ta kuma yi kira ga duk wanda aka taɓa yi wa fashin Adaidaita Sahu a kan hanyar Hotoro zuwa Dawakin Kudu da Wudil da ya tuntubi Sashen ’Yan Sandan Filin Hockey domin taimakawa wajen gano waɗanda ake zargin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending