Connect with us

News

Ba Ma Goyon Bayan Wata Jam’iyya Ko Ɗan Takara – Kungiyar ASUU

Published

on

ASUU logo 1000x600 1 768x461 (1)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya (ASUU) ta bayyana cewa ba ta goyon bayan wata jam’iyya ko ɗan takara gabanin babban zaɓen 2027, tare da gargaɗin ɗaukar mataki kan duk wanda ya yi amfani da sunanta wajen nuna goyon bayan siyasa.

Shugaban ƙungiyar, Christopher Piwuna, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin bikin tunawa da gwarazan ASUU na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.

Sama Da Mutum 50 Ne Suka Mutu Sakamakon  Arangamar ’Yan Bindiga Da ’Yan Sa-kai A Zamfara

Piwuna ya ce duk da cewa mambobin ƙungiyar na da ‘yancin zaɓar shugabannin da suke so da kuma shiga harkokin siyasa, ba su da izinin amfani da sunan ASUU wajen tallata wata jam’iyya ko ɗan takara.

 

Ya jaddada cewa ƙungiyar za ta ɗauki matakin ladabtarwa kan duk wani shugabanta da aka samu yana hulɗa da ‘yan siyasa ta hanyar da za ta sa a ɗauka cewa ASUU na goyon bayan wata jam’iyya.

Advertisement

“Ba ma goyon bayan wata jam’iyyar siyasa ko wani ɗan takara a ko’ina. Ba mu da hannu a siyasa, kuma za mu ci gaba da kasancewa haka,” in ji Piwuna.

Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan rahotannin cewa sama da manyan malaman jami’o’i 600 daga Arewacin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a watan Satumban 2026.

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending