Connect with us

Labarai

Dakarun Soji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da  Safarar Harsasai 300 A Kogi

Published

on

IMG 20261118 104033 468
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Rundunar Sojin Najeriya ta kama wani mutum mai shekaru 47 bisa zargin safarar harsasai, tare da ƙwato harsasai 300 na bindiga kirar 7.62 x 39mm a Jihar Kogi.

An kama wanda ake zargin ne a wani samame da sojojin rundunar Atsawa Blocking Force suka gudanar da misalin ƙarfe 9:30 na daren Talata, 17 ga Nuwamba, 2026.

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Wata Mata Da Wasu Mutum Uku Kan Zargin Kashe Yaron Kishiyarta Saboda Gado A Kano

Sojojin, tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai na yankin, sun cafke Umaru Muhammad, mazaunin ƙauyen Ashe, inda suka gano harsasan da aka ɓoye a cikin buhun wake.

Baya ga harsasan, jami’an tsaron sun kuma ƙwato babur kirar Bajaj, wayar hannu da kuma kuɗi har Naira 30,500 daga hannun wanda ake zargin.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin an shirya kai wa wasu mutane biyu, mai suna Gimba da Dare, harsasan, waɗanda ake cewa mazauna ƙauyen Gori ne da ke Ƙaramar Hukumar Lokoja, kusa da Kogin Neja.

Advertisement

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen biyu na aiki a matsayin ’yan banga a yankin, sai dai rundunar sojin ba ta tabbatar da wannan zargi ba.

Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken bayani kan lamarin da kuma sauran waɗanda ka iya kasancewa suna da hannu a safarar harsasan.

 

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending