News
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadiyyar Banka wa Kauye Wuta A Jigawa
An sake samun tashin hankali tsakanin manoma da makiyaya a jihar Jigawa, inda rikicin ya kai ga banka wa gidaje da injinan nika wuta, tare da kashe mutum ɗaya a kauyen Yelwan Musari, ƙaramar hukumar Guri, a ranar Asabar.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa mamacin manomin mai suna Magaji Mai’aya ya rasa ransa yayin da wasu da dama, ciki har da wani ɗan sanda, suka samu raunuka.
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadiyyar Banka wa Kauye Wuta A Jigawa
Wani manomi daga yankin, Ado Musa, ya ce makiyaya dauke da makamai sun kai farmaki kauyen daga ranar Asabar zuwa safiyar Lahadi, inda suka ƙone gidaje da injinan nika shinkafa na gargajiya.
“Makiyayan sun toshe hanyar Guri–Hadejia, suka hana a kai waɗanda suka jikkata asibitin Hadejia.
’Yan sanda da sojoji sun iso daga baya amma rikicin ya ci gaba, domin tun karfe rana bangarorin biyu ke arangama,” in ji shi.
Ba a tabbatar da adadin waɗanda suka jikkata daga ɓangaren makiyaya ba.
Rahotanni sun nuna cewa wannan sabon rikici ya samo asali ne daga tashin hankali da ya dade yana faruwa, tun bayan kashe wani manomi mai suna Ya’u Namara a bara.
Mazauna yankin sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa hukumomi sun yi ƙoƙarin sasanta bangarorin amma ba a samu mafita ba.
A cewar Musa, makiyaya sun daina zuwa kasuwannin yankin watanni da dama, wanda ya kara tsaurara zaman jama’a da ɗora hazo a tattaunawar sulhu.
Shugaban al’ummar makiyaya, Adamu Ori, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba domin jin ta bangarensu.
Sabon rikicin Guri ya zo ne ’yan kwanaki bayan wani makamancin rikici a kauyen Zarga, ƙaramar hukumar Taura, inda aka jikkata manoma 12.
Kakakin ’yan sandan jihar Jigawa, Lawan Adam, bai amsa kiraye-kirayen neman karin bayani ba.
Guri da wasu ƙananan hukumomi na arewa maso gabashin Jigawa na daga cikin wuraren da ke da filaye masu kyau don noma da kiwo.
Sai dai wannan albarka ta yi sanadin rikice-rikice masu tsawo, domin bangarorin biyu na takaddama kan ikon mallakar fili.
A wasu lokuta, zuwan makiyaya baƙi na yanayi-yanayi daga wasu jihohi ko ƙasashe kan ƙara hargitsa al’amura, wanda hakan ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.
Masu nazari na danganta rikice-rikicen yankin da matsalolin muhalli, tattalin arziki, tarihi da tsarin hulɗar al’umma, wadanda suka yi kamari tsawon shekaru.
