News
KANO: NUJ Ta Horar Da Yan Jaridu Hanyoyin Gujewa Fadawa Iftala’i Yayin Gudanar Da Aiki
Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kano ta gudanar da taron horaswa na yini guda domin ƙara ƙwarewar mambobinta kan batutuwan tsaro da bin ka’idojin aiki, a wani bangare na shagulgulan Press Week na shekarar 2025.
Taron, wanda aka yi a State Press Centre, ya kasance cikin jerin ayyukan da ƙungiyar ta shirya domin inganta aikin jarida da kuma tabbatar da cewa ’yan jarida suna da ilimin da ake buƙata wajen gudanar da aikinsu cikin tsaro.
KANO: NUJ Ta Horar Da Yan Jaridu Hanyoyin Gujewa Fadawa Iftala’i Yayin Gudanar Da Aiki
A jawabinsa, shugaban NUJ Kano, Comrade Sulaiman Abdullahi Dederi, ya ce an shirya taron ne domin sabunta ilimin ’yan jarida, tare da tunasar da su bin dokoki, ka’idoji da ladubban da ke jagorantar aikin jarida. Ya ce mahalarta sun fito daga gidajen rediyo, talabijin da jaridun yanar gizo a faɗin jihar.
Ya yi kira ga mahalarta da su yi amfani da sabon ilimin da suka samu domin ƙara inganta aikin jarida a Kano da ma Najeriya baki ɗaya. Ya kuma gode wa Gwamnatin Kano bisa goyon bayan da take bai wa ƙungiyar a kai a kai.
A bangare na musamman, Chief Press Secretary na Gidan Gwamnatin Kano, Mustafa Muhammad, ya gabatar da takarda kan muhimmancin kare kai daga fadawa iftila’i yayin gudanar da aiki, musamman idan ’yan jarida suke aiki a wuraren da ake iya fuskantar barazana ko tashe-tashen hankula.
Sauran masu gabatar da takardu sun haɗa da Adamu Salisu daga ofishin NBC Kano wanda ya yi bayani kan Code of Ethics na aikin jarida, da kuma gogaggiyar mawallafiya Amina Yahaya Deen wadda ta yi tsokaci kan dabarun fassara mai inganci a aikin jarida.
Akalla ’yan jarida 50 daga kafofin yaɗa labarai daban-daban ne suka halarci taron.
