Connect with us

Opinion

Ministan Tsaro Matawalle: ‘Yan Arewa, Dole Sai Mun Daina Yiwa Juna Hassada Sannan Allah Zai Tausaya Muna

Published

on

Spread the love

Daga Imam Murtadha Gusau

 

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

 

Advertisement

Assalamu alaikum

‘Yan uwana ‘yan arewa! Na dade ina fada cewa, wallahi, halin da muke ciki na rashin tsaro da talauci da sauran matsaloli, ba wani ne ya jawo muna ba illa halayen mu ne, da dabi’un mu marasa kyawo su suka jefa mu cikin halin da muke ciki, misali daga ciki shine, mummunan halin mu na yiwa juna hassada!

Babu wani Dan arewa da Allah Subhanahu zai yiwa wata baiwa ko wata daukaka ta shugabanci, ko arziki, ko ilimi, kai ko wace irin daukaka ce, face sai ka tarar ana yi masa hassada, ana yi masa bita da kulli, ana cin dunduniyarsa, ana neman a tadiye shi, ana neman sai an kai shi kasa.

Sanadiyyar wannan, sai muka wayi gari a cikin munmunan halin da muke ciki a yau.

Advertisement

 

Duk wanda ya shigo yankin kudancin kasar nan, wallahi ya sani, akwai tazarar arziki, ci gaba da zaman lafiya tsakanin su da arewa.

Gwamna Yusuf Ya Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Siyasantar Da Batun Tsaro, Yayin da Mahaddatan Qur’ani 4,444 Suka Gudanar Da Addu’o’i A Kano

Duk sauran yankunan kasar nan sun yi muna fintinkau, su wuce mu, sun tsere muna, sun bar mu a baya, ba domin komai ba, sai saboda halin mu na rashin kaunar junan mu da rashin son juna da yiwa juna hassada.

 

Advertisement

Abokan zaman mu ‘yan kudu, suna tare da ‘yan uwansu, suna kaunar su, suna goyon bayansu, amma mu ‘yan arewa, sam ba haka muke ba.

 

Babu abunda muka iya sai yiwa juna girman kai da dagawa, tare da raina juna da neman walakanta juna!

 

Advertisement

Kwanan nan, kotu ta yanke wa shugaban ‘yan ta’addan kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu hukunci, kuma dukkanin mu, mun san irin ta’addancin da yake yiwa kasar mu Najeriya da shugabanninta da ma ‘yan arewa. An kai shi gidan gyaran hali na Sokoto, amma nan take gwamnan jiharsa, ya dauki jirgin sama, ya tafi Sokoto tare da tawagar manyansu, suka ziyarci Nnamdi Kanu, suka lallashe shi, suka bashi hakuri, suka nuna masa cewa kar ya damu, suna tare da shi dari bisa dari.

 

Kuma har gobe, a can gidan gyaran halin, suna bibiyar lamarinsa. Suna taimakonsa. Sannan kusan dukkan manyan inyamurai da talakawansu suna tare da shi.

 

Advertisement

Kuma wannan hukunci da kotu ta yanke masa, hatta tsohon gwamna, kuma Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, wato Mista Peter Obi, sai da yayi magana akai, kuma ya nuna rashin jin dadin sa game da wannan hukunci.

 

Kowa yasan shugaban kungiyar ‘yan ta’adda na OPC, Mista Gani Adams. Kungiyar da Dokta Frederick Fasehun ya kafa a shekarar 1994, kafin ya mutu a shekarar 2017. A karkashin wannan kungiya, babu irin ta’addanci da Gani Adams bai yiwa Najeriya ba da ‘yan Arewa, amma bayan jagorancin wannan kungiyar, yau Gani Adams babban mutum ne sosai a cikin kabilar Yarbawa. Domin ma an bashi mukami babba, wanda duk wanda aka ba shi to ya kai babba, kuma jarumi. Yanzu shine Aare Ona Kakanfo na kasar Yarbawa baki daya.

 

Advertisement

Dukkanin mu muna da labarin Sunday Adeniyi Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, saboda Igbohon sunan garin sa ne. Sunday Igboho ba karamin Dan ta’adda bane wallahi. Yayi wa kasar nan ta’addanci da ‘yan arewa ba kadan ba. Sannan irin barnar da ya shuka wa hatta ‘yan uwansa ba kadan bane. Domin wallahi ya kashe rayuka marasa adadi a rikicin Ife da Modakeke da aka yi a shekarar 1997. Amma an wayi gari yau, Sunday Igboho ya zama babban mutum, kuma mai arziki a cikin kabilar Yarbawa baki daya.

 

An kama Sunday Igboho kwanakin baya, amma wallahi dukkanin manyan Yarbawa sai da suka sa baki aka sake shi.

 

Advertisement

Mujahid Dokubo Asari sananne ne a wurin mu. Duk da ta’addancin da yayiwa kasar nan da jami’an tsaron ta, bayan dimbin dukiya da ya mallaka, yau an wayi gari Mujahid Dokubo Asari babban Sarki ne a yankinsa da al’ummarsa na Kalabari, kuma mai fada aji.

 

Tompolo ma bai yi nisa da mu ba. Shi ma duk barnar da yayiwa kasar nan. Yau Tompolo ya zama hamshakin mai arziki, mai kudi ba na wasa ba!

 

Advertisement

Kai bayan duk anyi masu afuwa, har ma kwangiloli ake basu wai da sunan kula da tsaron ruwa da ke yankinsu.

 

Kwanakin baya, anyi wata gidauniya ta ci gaban ilimi a yankinsa, wallahi Tompolo shi kadai, kyautar naira biliyan goma ya bayar ga wannan gidauniya.

 

Advertisement

Ba su kadai ba, kai in dai takaice maka wannan labari, wallahi, wallahi, wallahi dukkanin tsofaffin ‘yan ta’addar Naija Delta, wadanda Marigayi Umaru Musa ‘Yaradua yayi wa afuwa, dukkaninsu a halin yanzu sun zama manyan mutane, kuma sun kudance!

 

Amma sabanin mu ‘yan arewa, duk wanda aka ba wa mukami ko wani matsayi, ko Allah yayi masa wata daukaka, hankalin mu ba zai kwanta ba, har sai mun ga an cire shi. Sai mun ga an walakanta shi, sai mun ga ya tozarta, sannan hankalin mu zai kwanta.

 

Advertisement

Tsohon ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ‘yan arewa ne suka yi kutun-kutun sai da aka cire shi. Maganar cewa ya sauka ne saboda hali na rashin lafiya, wannan ba gaskiya bane wallahi.

 

To yanzu ba shike nan ba, an cire Badaru, hankalin mu ya kwanta!

 

Advertisement

Shi kan sa sabon da aka nada yanzu, wato Christopher Musa, naji wasu ‘yan arewan su fara cece-kuce da surutu akan sa.

 

Ai ba zamu daina ba, saboda duniya ta shaida wannan halin mu ne. Bamu da aiki sai kin namu!

 

Advertisement

Har mai bai wa Shugaban kasa shawara akan sha’anin tsaro, wato Nuhu Ribadu, shi ma naji mahassada sun sako shi a gaba, wai sai an cire shi. Haba jama’ah, wai don Allah mu wadanne irin mutane ne? Wace al’ummah ce wannan?

 

Ku duba ku gani, saboda wadannan halaye namu na hassada, an wayi gari ‘yan arewa mun zama abun dariya, mun zama abun tausayi a kasar nan. Duk anyi muna fintinkau.

 

Advertisement

Yanzu domin Allah, da aka cire Badaru wace irin riba muka samu? Sannan yanzu idan an cire Matawalle, ko Nuhu Ribadu, don Allah wace irin riba zamu amfana da ita?

 

Wallahi, wallahi, wallahi ya zama wajibi, muddin muna so Allah ya tausaya muna, ya fitar damu cikin kangin da muke ciki, sai mun daina yiwa junan mu hassada, sai mun so juna, sai mun rungumi juna, sai mun ba juna goyon baya, sai mun yiwa junan mu addu’o’i da rokon Allah da fatan alkhairi. Idan ba haka ba kuwa, to matsaloli yanzu muka fara ganinsu, Allah ya sawwake, amin.

 

Advertisement

Ku sani, hassada ita ce, mutum yayi fata, ko yaso gushewar wata ni’ima ko wata baiwa, ko wata daukaka, ko wani matsayi, ko dai na duniya ko na addini, da Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi ma wani mutum daga cikin bayinsa. Wato dai ya kasance a wayi gari, mutum yana bakin ciki ko jin haushi ga wata baiwa da Allah Madaukaki ya ba wani, ko dai a fagen duniya ko kuma a fagen addini, tare da fatan ni’imar ta dawo gare shi, koma ba ta dawo gare shi ba. Burinsa dai shine wancan da yake ma hassadar ya rasa. Ko kuma in ce ta gushe kowa ya rasa!

 

Jama’ah hassada wallahi mugun ciwo ce, kuma ba ta da kyau. Kuma mafi yawan matsalolin da muka samu kan mu ciki a yau a arewa, sun samo asali ne daga hassada.

 

Advertisement

Ya kai mai hassada, ka sani, wallahi jin dadin wani baya rage naka jin dadin, lafiyar wani bata cutar da kai, Kuma arzikin wani baya talautaka, to idan haka ne, don Allah menene na hassada?

 

Ka sani, komai fa na Allah ne, kuma shi yake rabawa. Ka sani, ko ka mutu ba zan samu rabonka ba, haka nima in na mutu ba za’a baka rabo na ba. Kowa iya abinda aka rubuta masa shi zai samu a rayuwarsa. Babu mai iya cin rabon wani.

 

Advertisement

Kuma ka sani, tabbas, hakika, Allah baya kuskure, kuma ba’a yiwa Allah tilas.. Don haka mu bi rayuwar nan a hankali, mu natsu mu kwantar da hankalin mu game da abinda yake faruwa da mu… Mu sani ba mai iya canza hukuncin Allah.

 

Mukamin ministan tsaro, Allah ne ya nufi a bai wa Matawalle, idan kuma kace ba haka ba, to kana so kaci Allah gyara kenan!

 

Advertisement

Wallahi wannan surutai da hayaniya da kuke tayi akan mukamin minista da Allah ya dora Matawalle, ku sani, ba da shi kuke ja ba fa, wallahi kuna ja ne da Allah, domin Matawalle ba shine ya nada kan sa ba, ya zama minista ne da sanin Allah, da yardar Allah, kuma da amincewarsa.

 

Don haka, wallahi, kuji tsoron Allah, kuma ku shiga taitayinku. Domin babu wani mahaluki da zai ja da Allah yaci nasara!

 

Advertisement

Kuma ni a matsayina na Musulmi, wanda yayi imani da Allah da Manzonsa (SAW). Kuma nayi imani da kasancewar Alkur’ani mai girma zancen Allah ne. To na yarda da rantsuwar da Matawalle yayi da Alkur’ani, cewa shi baya goyon bayan ta’addanci da ‘yan ta’adda!

 

Duk duniya ta shaida wannan rantsuwa da Matawalle yayi. Don haka, duk wanda bai yarda da Alkur’ani ba, wannan shi ya sani, kuma da shi da Allah.

 

Advertisement

Amma ni dai kam, na yarda da wannan rantsuwa da Matawalle yayi. Duk wanda bai yarda ba kuwa, to ya rike ra’ayinsa ya bar ni da nawa!

 

Sannan kuma dadin abun shine, duk zamu hadu a gaban Allah Subhanahu wa Ta’ala, domin yayi hukunci tsakaninmu.

 

Advertisement

Kuma daga karshe, mu sani, ita siyasa fa ba hauka bace. Kar mu zo muna Kalubalantar hukuncin Allah, saboda son mu cimma wani buri namu na siyasa, ko wani buri na son zuciya da sunan siyasa!

 

Ya Allah, ka raba mu da cutar hassada, ka bamu sanyin zuciya da tawakkali da karfin zuciyar yarda da kaddarar Allah.

 

Advertisement

Ya Allah, kar ka sa mu cikin masu jayayya da hukuncinka, amin Ya Hayyu Ya Qayyum.

 

Wassalamu alaikum,

 

Advertisement

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuto, daga Okene, jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *