Connect with us

News

Gwamna Yusuf Ya Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Siyasantar Da Batun Tsaro, Yayin da Mahaddatan Qur’ani 4,444 Suka Gudanar Da Addu’o’i A Kano

Published

on

1765110805948
Spread the love

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargadi ‘Yan Najeriya da su guji siyasantar da batun tsaro, yana mai jaddada cewa barazanar ‘Yan bindiga ba ta tantance jam’iyya ko ra’ayin siyasa.

Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a ranar Asabar, yayin wani taron addu’a da karatun Al-Qur’ani Mai Girma da aka gudanar a Fadar Gwamnati ta Kano, inda mahaddatan Qur’ani 4,444 suka taru domin neman taimakon Allah kan matsalar hare-haren ‘Yan bindiga da aka samu a kwanakin baya Wasu yankuna na Jihar.

Fadar Mulkin Jamhuriyar Benin Ta Ce An Dakile Yunkurin Juyin Mulki A Kasar

Taron ya samu halartar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, tare da manyan jami’an gwamnati, malamai da shugabannin addini na ciki da wajen Jihar Kano

Advertisement

Gwamna Yusuf ya jaddada cewa matsalar tsaro “ba ta san siyasa ko jam’iyya ba,” yana kira ga kowa da kowa da a hade kai wajen yakar ta,

“Mun so mu ga kowa yana hada hannu wajen kawar da wannan matsala domin mu kubutar da Kano,” in ji shi.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ci gaba da samar wa hukumomin tsaro kayayyakin aiki da suke bukata, tare da kasancewa a kai a kai cikin tattaunawa da su domin gano sabbin bukatu.

Advertisement

Gwamnan ya bukaci al’umma su kwantar da hankalinsu, yana tabbatar masu cewa gwamnati da hukumomin tsaro na aiki dare da rana domin kare Kano da kewaye.

Ya Kuma ce taron addu’ar ba wai kashe kudi ba ne kawai, illa kuwa wani “zuba jari na ruhaniya” da ya kamata kowane nagarin dan Kano ya tallafa.

A nasa jawabin, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yaba wa gwamnatin jihar bisa shirya wannan babban taron addu’a, yana mai cewa mataki ne “mai karfin gwiwa kuma a kan lokaci”.

Advertisement

Ya ce a yayin ziyararsa ta kwanan nan a kauyen Faruruwa a Karamar Hukumar Shanono, ya ga sabbin hanyoyin karkara da gwamnatin jihar ke ginawa.

A cewarsa irin wannan gina hanyoyi zai taimaka matuka wajen hanzarta amsa kiran gaggawa a yankunan da ke da nisa, abin da zai karfafa tsaro.

Sarkin ya kuma yi kira da a tabbatar da cewa kananan hukumomi na ci gaba da amfana da muhimman tituna da za su hade su sosai da sauran sassan jihar.

Advertisement

Ya Kara tabbatar wa gwamnan cewa Majalisar Masarautar Kano za ta ci gaba da mara wa gwamnati baya wajen dawo da martabar Kano a matsayin cibiyar zaman lafiya hadin kai da kasuwanci.

Taron ya kunshi addu’o’i da karatun Al-Qur’ani daga malamai da mahaddata da suka fito daga dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *