Opinion
Dalilan Da Ya Sa Gwamna Abba Ya Kamata Ya Zabi Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Sa
DAGA BALARABE IBRAHIM SULAIMAN
Bayan kammala sauyin jam’iyyar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, daga NNPP zuwa APC, muhawara na ci gaba da karfi kan yadda za a sake tsara tafiyar gwamnati domin dacewa da sabon yanayin siyasa a jihar.
Rahotanni na nuni da cewa gwamnan na shirye-shiryen yin garambawul (reshuffle) a majalisar zartarwar Jihar nan gaba kadan, biyo bayan murabus din wasu ‘yan majalisar zartarwa da suka zabi Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran tafiyar Kwankwasiyya.
Karancin Maganin Dafin Maciji Na Kara Jefa Rayukan Jama’a Cikin Hadari A Najeriya
Masu sharhi kan siyasa sun ce cike guraben da suka samu gibi na da muhimmanci wajen tabbatar da ci gaba da tafiyar da gwamnati ba tare da tsaiko ba.
A wannan sabon yanayi, ana hasashen cewa ofishin mataimakin gwamna ma na iya fuskantar sauyi domin samar da daidaito da hadin kai a sabuwar jam’iyya.
A cikin sunayen da ke yawo a fagen tattaunawa akwai Honarabul Murtala Sule Garo, wanda wasu masu ruwa da tsaki ke ganin yana da gogewa a harkokin mulki da kuma karbuwa a matakin kasa.
Murtala Sule Garo ya taba rike mukamin Kwamishinan Kananan Hukumomi a jihar Kano, inda ya mayar da hankali kan ci gaban karkara, ilimi da kuma tafiyar da harkokin gwamnati cikin gaskiya, a cewar masu goyon bayansa.
Ana kuma kallon Garo a matsayin dan siyasa mai tushe a kasa, wanda ke da damar hada matasa da al’umma a fadin kananan hukumomi 44 na jihar, lamarin da ake ganin na iya taimakawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali a sabon tsarin siyasa.
Wasu masana siyasa sun kuma yi nuni da cewa kasancewarsa daga Kano ta Arewa na iya taimakawa wajen samar da daidaiton yankuna a shugabancin jihar, tare da kasancewarsa gada tsakanin tsoffin tsarin siyasa da sabbin dabarun APC.
A halin yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar Kano kan sunan wanda za a nada a matsayin mataimakin gwamna, sai dai ana sa ran karin bayani zai fito ne bayan sanar da sabon tsarin majalisar zartarwa.
