Connect with us

Politics

‎Siyasata Ta Zo Karshe, In Har Fubara Ya Yi Nasara A Wa’adi Na Biyu. Don Haka, Ba Zan Yarda Na Binne Kaina Ba. ‎—Nyesom Wike

Published

on

Spread the love

Rikicin siyasar Jihar Rivers na ƙara kamari, yayin da bangarori biyu masu ƙarfin fada-a-ji ke ci gaba da ja-in-ja kan makomar shugabancin jihar, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

‎Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa siyasarsa za ta zo ƙarshe matuƙar Gwamna Siminalayi Fubara ya samu nasarar lashe wa’adi na biyu.

An Sayar Da Kifi Mai Nauyin Kilogiram 240 A Kan Naira Biliyan 4.5

‎“Siyasata ta zo ƙarshe, in har Fubara ya yi nasara a wa’adi na biyu. Don haka, ba zan yarda na binne kaina ba,” in ji Wike.

‎Masana harkokin siyasa na danganta rikicin da ke ƙara tsananta a Rivers da rigimar iko da tasiri, wadda ke da alaƙa kai tsaye da shirye-shiryen zaɓen 2027, inda manyan ‘yan siyasa daga matakin jiha da na tarayya ke ci gaba da nuna bangaranci.‎

Advertisement

‎Tun farko, rikicin ya ta’allaka ne kan tsarin siyasa (political structure) na jihar, musamman a matakin kananan hukumomi—wani ginshiƙi da ke zama muhimmin tubali ga kowanne ɗan siyasa a Rivers.

Sai dai a yanzu, rikicin ya bayyana karara a matsayin takaddamar wa ke da ikon fitar da ɗan takarar gwamna a 2027.

‎Wata ‘yar jarida kuma mai sharhi kan siyasa, Oby Ndukwe, ta bayyana cewa duk lokacin da mutum ya kai wani matsayi, “akan fara ganin ‘yan ba-ni-na-yi da masu ba da shawara masu nasu manufofi, wanda hakan ke ƙara rikita al’amura.”

‎Rikicin siyasar Rivers ya samo asali ne tun shekarar 2023, wanda ya kai ga ayyana dokar ta-baci, da kuma yunƙurin sulhu bayan haka. Sai dai dukkan matakan ba su haifar da daidaito ba.

Advertisement

‎Wike na dagewa cewa an cimma yarjejeniya da ke tanadin cewa Gwamna Fubara ba zai sake tsayawa takara a 2027 ba, har ma ya yi barazanar wallafa yarjejeniyar a jaridu domin duniya ta gani.

‎Sai dai Gwamna Fubara, wanda daga bisani ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, ya yi watsi da ikirarin yarjejeniyar, yana mai cewa babu wani da zai hana shi tsayawa takara. Matakin ya ƙara fusata magoya bayan Wike da shi kansa Wiken.

‎Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Rivers, Rt. Hon. Martins Amaewhule, wanda ke goyon bayan Wike, ya ce wasu kalaman baya-bayan nan na Gwamna Fubara ne suka tilasta musu bayyana matsayinsu ga manema labarai.

‎A cewarsa, “Nyesom Wike masoyin Rivers ne, mai son zaman lafiya da cigaban jihar.”

Advertisement

‎A gefe guda, Gwamna Fubara ya ci gaba da ƙarfafa sahun magoya bayansa, inda ya bayyana cewa irin wadannan taruka na taimaka musu wajen tantance “waɗanda ke tare da su da kuma waɗanda ba sa tare da su.”

‎Rahotanni na nuna cewa shugabannin jam’iyyar APC a matakin jiha da ƙasa, tare da yawancin gwamnonin APC—kimanin 30—sun nuna goyon baya ga Fubara domin sake tsayawa takara.

‎Wike ya bayyana wannan mataki a matsayin yunƙurin binne shi da siyasa, yana mai cewa ba zai mika wuya ba.

‎ “Ba yau muka fara wannan yaƙi ba—ko a matakin jiha ko ƙasa. Ba wanda za a bari ya fi mu ƙarfi saboda kawai an ba shi dama,” in ji Wike.

Advertisement

‎Rikicin siyasar ya fara yin tasiri kan harkokin mulki, musamman batun kasafin kuɗin ƙarin kashe kuɗi (supplementary budget) da kuma kasafin 2026, ganin yadda yawancin ‘yan majalisar da ke da ikon sahale kasafin ke biyayya ga bangaren Wike.

‎A wani yunƙuri na sake haɗa karfi, Nyesom Wike ya kaddamar da rangadin kananan hukumomi 23 na jihar Rivers, matakin da masu lura da al’amura ke kallon shi a matsayin dabarar sake haɗa magoya bayansa da kuma shirya gabanin fafatawar siyasar da ke tafe.

DW

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *