Connect with us

Interview

Kansilan Shahuci Ya Taya Gwamnan Kano Murnar Cika Shekaru 63, Ya Yaba da Jagorancinsa

Published

on

IMG 20260109 WA0004
Spread the love

Kansilan mazabar Shahuci kuma Shugaban Kansiloli na Ƙaramar Hukumar Birnin Kano (Kano Municipal), Hon. Yahya Abdullahi, wanda aka fi sani da Baba Mai Duniya, ya taya Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, murnar cika shekaru 63 a duniya.

Hon. Abdullahi ya bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin shugaba nagari, mai kishin talakawa, tausayi da jajircewa wajen kawo sauyi mai ma’ana a rayuwar al’ummar jihar Kano.

‎’Yan Majalisar Dokokin Kano Sun Goyi Bayan Shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Ficewa Daga NNPP Zuwa APC ‎

Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwar taya murna da ya fitar, inda ya ce al’ummar Kano sun yi babban sa’a da samun shugaba irin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya san darajar jama’arsa tare da fifita cigabansu.

“Tabbas Kano na cikin alheri da samun irin wannan gwamna, domin ba kasafai ake samun shugaba mai hangen nesa, jajircewa da tsantsar niyyar yi wa jama’a aiki ba,” in ji Hon. Abdullahi.

Advertisement

Ya ƙara da cewa salon mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bambanta da na takwarorinsa a fadin Najeriya, musamman wajen mayar da hankali kan walwalar al’umma, ci gaban ilimi, lafiya da samar da ayyukan more rayuwa.

A sakon nasa, Hon. Abdullahi ya yi kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da bai wa gwamnan cikakken hadin kai, domin tabbatar da dorewar ayyukan alheri da gina ingantaccen shugabanci mai amfani ga kowa.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *