News
Duk Da Gargadi, Jama’a Sun Yi Tururuwa Dibar Ganimar Man Dizel Bayan Tanka Ta Fadi A Legas
Tanka mai ɗauke da dizal ta kife a gadar Tincan Liverpool da ke yankin Apapa a jihar Legas, inda wasu mazauna unguwa da masu wucewa suka rika kwashe man da ya zube.
Lamarin ya faru da sassafe a ranar Litinin a lokacin cunkoson safiya. Shaidun gani da ido sun ce jami’an kula da zirga-zirga ba su kai wurin nan take ba.
Iran Ta Sha Alwashin Gwabza Yaƙi Da Duk Ƙasar Da Ta Yi Gangancin Kai Mata Hari
Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ta ce an rufe gadar na ɗan lokaci, amma daga baya an sake buɗe ta bayan jami’an kashe gobara sun rage haɗarin man da ya zube.
Hukumar ta ƙara da cewa zirga-zirga na inganta yayin da ake jiran motar ɗaukar tankar.
Hukumar ta kuma gargadi jama’a kan haɗarin irin wannan hali, tana tunatar da mummunan sakamakon da ya faru a baya a sassan ƙasar, inda mutane da dama suka rasa rayukansu yayin ƙoƙarin kwashe mai daga tankoki da suka kife.
