News
Jami’an ’Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Bisa Zargin Kashe Matarsa A Kebbi
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta sanar da cafke wani mutum mai suna Sule Gurmu, wanda ake zargi da kashe matarsa, Umaima Maidawa, mai shekaru 25, a wani lamari da ake alakanta da rikicin da ya faru a cikin gida su a garin Bayawa, da ke karamar hukumar Augie.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar 13 ga Janairu, 2026, inda ake zargin mijin ya buge matarsa ne da fartanya yayin da suka samu sabani.
Kisan Gilla: Shawarwari Ga Mata Masu Zaman Gida Don Kare Rayukansu
A cewar ’yan sanda, Umaima ta rasu jim kadan bayan harin, lamarin da ya janyo fara bincike daga hukumomin tsaro.
Bayan faruwar lamarin, wanda ake zargin ya tsere daga garin Bayawa, amma daga bisani jami’an tsaro suka gano shi tare da cafke shi a garin Katami, da ke karamar hukumar Silame a Jihar Sakkwato.
An ce aikin cafke shi ya samu nasara ne bayan umarnin da Shugaban Karamar Hukumar Augie, Yahaya Augie, ya bayar, inda ya bukaci hukumomin tsaro su kama shi cikin gaggawa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da cafke wanda ake zargin.
“Mun kama wanda ake zargin, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike,” in ji shi.
PUNCH
