News
Kisan Gilla: Shawarwari Ga Mata Masu Zaman Gida Don Kare Rayukansu
A wasu sassan Jihar Kano, fargaba na ci gaba da yaduwa a tsakanin al’umma, musamman mata masu zaman gida, sakamakon rahotannin kisan gilla da ake samu a ‘yan kwanakin nan.
Mazauna wasu unguwanni sun bayyana cewa lamarin ya sa mutane da dama suka fara sauya salon rayuwarsu, musamman ta fuskar tsaro da kula da muhallinsu.
Wata mata da ke zaune a yankin Hotoro, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce tun bayan samun labaran hare-hare, ta ƙara tsaurara matakan tsaro a gidanta.
“Yanzu ba ma sake buɗe ƙofa kai-tsaye. Sai mun tabbatar da wanda ke kwankwasa. Ko yaro ne, dole sai an yi bincike,” in ji ta.
Rahotanni na nuni da cewa irin wannan matakan na iya rage haɗarin fadawa hannun masu aikata laifuka.
Daga cikin shawarwarin da suke bayarwa ga mata akwai kulle ƙofofi da tagogi da kyau, guje wa barin abubuwa masu haɗari a fili, da kuma koyon dabarun kare kai..
Wani masani kan harkokin tsaro ya bayyana cewa koyon self-defence ba wai don kai farmaki ba ne, illa domin samun damar tsira idan aka samu barazana.
“Babban buri shi ne tsira, ba faɗa ba,” in ji shi.
Haka kuma, ana kira ga mata da su kasance da hanyar kiran gaggawa a kowane lokaci, ta hanyar barin kati a wayoyinsu ko da na kuɗi kaɗan ne, domin neman taimako idan bukatar hakan ta taso.
Wasu mazauna unguwannin sun ce yin ihu idan an fuskanci hatsari na daga cikin hanyoyin da ke jawo hankalin maƙwabta, lamarin da kan hana masu laifi cimma burinsu.
Baya ga matakan tsaro na zahiri, mata da dama sun ce sun fi maida hankali kan addu’o’i da ambaton Allah, suna mai cewa hakan na basu kwanciyar hankali da ƙarfin guiwa.
Masana sun ce haɗa tsaro na zahiri da na ruhi na daga cikin muhimman matakan da za su iya taimaka wa mata su tsira a wannan yanayi da ake ciki.
