News
An Yi Arangama Tsakanin Jami’an Tsaro Da Masu Zanga-zanga A Birnin Los Angeles
A safiyar Lahadin da ta gabata ne aka wayi gari da jibge dimbin jami’an tsaro a sassa daban-daban na birnin Los Angeles, bayan samun rahoton cewa masu zanga-zanga za su gudanar da taruka da gangamin nuna damuwa a fadin birnin.
Rahotanni sun bayyana cewa, kimanin jami’an tsaro 300 ne aka tura domin dakile yunkurin masu zanga-zangar da suka cika tituna, tare da gudanar da farautar wadanda ake zargi da karya doka a wuraren kasuwanci, hanyoyi da kuma harabar kotuna.
Ɓarawon Waya Yayi Sanadiyyar Mutuwar Babban Jami’in Soja A Kaduna
Wani ganau da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “Zamu ci gaba da kare ‘yancinmu na walwala da kare al’ummarmu, ko da hakan na nufin fuskantar feshin hayaki ko raunata.”
A yayin da tarzomar ke kara kazancewa, Gwamnan jihar California, Gavin Newsom, wanda dan jam’iyyar Democrat ne, ya caccaki shugaba Donald Trump bisa matakin da ya dauka, yana mai cewa: “Wannan mataki da Shugaban kasa ya dauka alama ce ta rashin imani da kyautatawa ’yan kasa.”
A daren Asabar ne aka fara rikicin da ya jawo fargaba da rudani a cikin birnin Los Angeles, bayan da jami’an tsaro suka kai samame a wasu yankuna, inda suka cafke mutane fiye da 40 bisa zargin karya dokokin shige da fice.
An samu munin arangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga musamman a yankin Paramount, da ke kudu maso gabashin Los Angeles, inda jami’an suka harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa taron, yayin da masu zanga-zangar ke rokon jami’an kwastam da na shige da fice da su bar yankin su.
Masu sharhi na ganin cewa rikicin na iya ci gaba da kazancewa muddin ba a nemo hanyar sasanci ba, musamman idan aka ci gaba da fatali da kiran janye rundunonin tsaro daga wuraren da jama’a ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum
