News
Hadimin Shugaba Tinubu Yayi Murabus Daga Mukaminsa
Aliyu Audu, mai taimaka wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na musamman kan harkokin jama’a, ya ajiye aikinsa daga mukaminsa a hukumance.
A cikin wata wasika mai shafi ɗaya da aka sanya wa hannu a ranar 8 ga Yuni, wacce aka miƙa ta hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Audu ya bayyana cewa: “Ina rubuto wannan wasika domin in sanar da ajiye aikina daga wannan matsayi aikin nan take.”
Buratai Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Harin Boko Haram A Borno
Audu ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa damar da ya ba shi na yin hidima ga ƙasa ƙarƙashin gwamnatin sa.
Haka kuma, ya jinjina wa tsohon mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, wanda ya ba da shawarar da ta kai ga naɗinsa a matsayin mai taimaka wa shugaban ƙasa na musamman.
An naɗa Aliyu Audu a hukumance a ranar 9 ga Oktoba, 2023, bayan amincewar Shugaba Tinubu da nadin nasa, wanda aka fara tun bayan shawarar da aka bayar a ranar 26 ga Agusta, 2023.
Har zuwa lokacin da ake kammala wannan rahoto, babu wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa dangane da murabus ɗin Audu.
