Business
Kamfanin First Class Refreshment Limited Ya Samu Lasisin Kasuwanci A Saudiyya
Kamfanin First Class Refreshment Limited na Nijeriya ya samu lasisin gudanar da kasuwanci (franchise) daga kamfanin Silk United Company na kasar Saudiyya, a wani mataki da ake ganin zai ƙara ƙarfafa alaƙar cinikayya tsakanin ƙasashen biyu.
Babban Daraktan Kamfanin First Class Group, Dr. Shuaibu Burji, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Laraba a Kaduna.
Burkina Faso Ta Saki Sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10
A cewarsa, yarjejeniyar da aka kulla a birnin Riyadh ta bai wa First Class Refreshment damar aiwatar da tsarin kasuwancin Silk United a Nijeriya, inda Lagos za ta kasance cibiyar gudanar da akan talla, rarrabawa da sauƙaƙa harkokin kasuwanci.
Dr. Burji ya ce, a karkashin wannan tsari, kamfanin zai rika tallata da rarraba kayayyakin Saudiyya masu inganci da ba na man fetur ba a kasuwar Nijeriya, tare da kula da harkokin jigila, shigo da kaya da sauƙaƙa hanyoyin kasuwanci.
Ya kara da cewa ana sa ran wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen inganta tsarin shigo da kaya da fitar da su a Nijeriya, tare da samar da damar samun kayayyakin da suka samu sahalewar ƙasa da ƙasa, lamarin da zai ƙara amincewar masu saye.
Shugaban kamfanin ya bayyana cewa wannan nasara ta yi daidai da burin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, musamman ta hanyar ƙarfafa cinikayya da rage dogaro da man fetur.
Ya kuma ce First Class Refreshment, wadda ke da sahalewar Authorised Economic Operator (AEO), na da shirin faɗaɗa ayyukanta zuwa kasuwannin duniya, ciki har da fitar da kayan ciye-ciyen gargajiyar Nijeriya zuwa ƙasashen waje.
Dr. Burji ya ƙara da cewa wannan shiri ya dace da Manufar Saudiyya ta Vision 2030, wadda ke mayar da hankali kan bunƙasar tattalin arziki da ƙarfafa alaƙar kasuwanci da ƙasashen waje.
A cewarsa, ana sa ran ofishin kamfanin da ke Lagos zai fara aiki nan gaba kaɗan, inda ake tsammanin zai taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa kasuwancin ƙetare da dangantakar tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Saudiyya.
(NAN)
