Connect with us

News

‎Burkina Faso Ta Saki Sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya da ta tsare na tsawon kwanaki 10, biyo bayan tsoma bakin diflomasiyya da gwamnatin Najeriya ta yi, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar ta tabbatar.

‎Sakin sojojin ya biyo bayan wata ganawa da tawagar gwamnatin Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ta yi da shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, a ranar Laraba, 17 ga Disamba, 2025.

Kotu Ta Ba Wa NDLEA Damar Tsare Jirgin Ruwa Da Ma’aikatansa 21

‎A cewar ma’aikatar, gwamnatin Najeriya ta nemi afuwa a hukumance kan keta sararin samaniyar Burkina Faso, lamarin da ya janyo tsare sojojin da jirginsu.

‎Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya shaida wa Jaridar Punch a daren Laraba cewa an kammala sakin sojojin.

‎ “An saki sojojin. Na tabbatar da hakan daga Shugaban Ofishin Jakadancinmu a Burkina Faso,” in ji shi.

‎Sai dai har yanzu ba a bayyana takamaiman lokacin da sojojin za su dawo Najeriya ba, domin shirye-shiryen tafiyarsu ba su kammala bayyana ba.

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending