Connect with us

News

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Da Kwamishinan Jin-ƙai Kibiya Sun Karɓi Lambar Yabo

Published

on

IMG 20251218 WA0021

Ƙungiyar Centre for Human Rights and Charity Development Association (CHRCDA) ta bai wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Alhaji Adamu Ali Kibiya, Lambar Yabo ta Ƙwarewa, bisa ayyukan jin-ƙai da suka aiwatar a faɗin jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ibrahim Abdullahi, ANIPR, Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Harkokin Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, ya sanya wa hannu.

‎Kamfanin First Class Refreshment Limited Ya Samu Lasisin Kasuwanci A Saudiyya

An miƙa lambar yabon ne a ranar Alhamis a ofishin Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai, inda Darakta Janar na ƙungiyar, Kamarad Auwal Jibril Maifada, ya bayyana cewa an bayar da wannan karramawa ne domin yaba wa jajircewar shugabannin biyu wajen aiwatar da shirye-shiryen da ke inganta rayuwar al’ummar Jihar Kano.

Maifada ya ce tun bayan zuwan wannan gwamnati, an gyara hanyoyi da dama, lamarin da ya ƙara bunƙasa harkokin tattalin arziƙi tare da rage lokacin tafiye-tafiye sakamakon ingantacciyar zirga-zirgar ababen hawa da masu tafiya a ƙasa.

Ya kuma jaddada tausayin Gwamna Abba Kabir Yusuf ga mata, yara da sauran masu rauni a cikin al’umma, yana mai bayyana hakan a matsayin muhimmin dalilin bayar da lambar yabon.

A cewarsa, yadda gwamnan ke amsa korafe-korafen jama’a cikin gaggawa da tausayi ya sa gwamnatin ta samu karɓuwa a zukatan al’umma.

Advertisement

Daraktan Janar na CHRCDA ya kuma ambaci biyan basussukan alawus na mutuwa da garatuti da aka dade ana bi a baya a matsayin hujja ta shugabanci mai cike da tausayi da la’akari da jama’a.

Haka zalika, Maifada ya yabawa Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai bisa yadda yake cike gibin ƙoƙarin gwamna ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen jin-ƙai daban-daban a faɗin jihar, bisa tsarin manufofin ƙungiyar.

Da yake mayar da martani a madadin ma’aikatar, Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Alhaji Adamu Ali Kibiya, ya nuna godiya ga ƙungiyar bisa ganin sun cancanci wannan karramawa, yana mai bayyana lambar yabon a matsayin ƙarfafawa da za ta sa a ƙara kaimi wajen ayyukan jin-ƙai.

Ya ce samun shugaba nagari mai gaskiya da kishin jama’a kamar Gwamna Abba Kabir Yusuf wata babbar ni’ima ce ga Jihar Kano, yana mai cewa tsarin shugabancin gwamnan na ci gaba da haifar da sakamako mai kyau.

Kwamishinan ya kara da cewa samun irin wannan yabo na ƙarfafa gwiwa, yana mai tabbatar da cewa ma’aikatar tare da gwamnatin jihar za su ci gaba da faɗaɗa shirye-shiryen jin-ƙai domin amfanin jama’a

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending